Kalli hotunan 'yan Manchester United da za su kara da City

'Yan wasan Manchester United sun yi atisaye gabanin karawar da za su yi da makwabtansu, Manchester City ranar Asabar.

City ce ta daya a saman teburin gasar Firimiya ta Ingila, yayin da United ke biye da ita.

Hakkin mallakar hoto manutd.com
Image caption Duka 'yan wasan United sun yi atisaye idan ban da Sergio Romero wanda ke fama da rauni
Hakkin mallakar hoto manutd.com
Image caption Alexis Sanchez ya shirya tsaf domin buga wasan hamayyar a karon farko tun bayan da ya koma United
Hakkin mallakar hoto manutd.com
Image caption City za ta lashe kofin Firimiya idan ta samu nasara a kan United
Hakkin mallakar hoto manutd.com
Image caption Romelu Lukaku na kan ganiyarsa inda ya ke ruwan kwallaye tun daga watan Janairu
Hakkin mallakar hoto manutd.com
Image caption Wasu na ganin United ta samu kwarin gwuiwa saboda ganin yadda Liverpool ta casa Man City a gasar Zakarun Turai
Hakkin mallakar hoto manutd.com
Image caption Amma 'yan wasan United sun kwana da sanin cewa wannan ba abin dogaro ba ne
Hakkin mallakar hoto manutd.com
Image caption Musamman ganin yadda sau daya City ta yi rashin nasara a gasar ta Firimiyar bana
Hakkin mallakar hoto manutd.com
Image caption United na bukatar 'yan wasa irinsu Paul Pogba su shana idan har ta son doke City
Hakkin mallakar hoto manutd.com
Image caption A wasan farko da suka kara City ta doke United da ci 2-1 har gida
Hakkin mallakar hoto manutd.com
Image caption A yanzu suna fatan ganin sun rama
Hakkin mallakar hoto manutd.com
Image caption Jose Mourinho ya ce burinsa shi ne United ta kare a mataki na biyu
Hakkin mallakar hoto manutd.com
Image caption Jesse Lingard yana taka rawa sosai a kakar bana