An yi wa Manchester City tayin sayen Paul Pogba

Paul Pogba and Henrikh Mkhitaryan
Bayanan hoto,

Mkhitaryan ya koma Arsenal a watan Janairu

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce an yi masa tayin sayen Paul Pogba da Henrikh Mkhitaryan daga Manchester United a watan Janairun da ya wuce.

Guardiola ya ce wakilin 'yan wasan, Mino Raiola, ya tuntube shi inda ya gaya masa cewa a shirye 'yan wasan su ke su bar United.

Pogba, wanda ya zo United a matsayin wanda ya fi kowa tsada a wancan lokacin kan fam miliyan 89 a 2016, ya ci gaba da zama a Old Trafford yayin da Mkhitaryan ya koma Arsenal.

Raiola ya shaida wa BBC cewa bai yi magana da Guardiola ba sai dai bai musanta cewa ya shaida wa City cewa 'yan wasan na son sauya kulob ba.

United sun ce ba abu ne mai yiwuwa ba su sayar da Pogba ga City.

Bayanan hoto,

Jim kadan bayan fitowar labarin sai Pogba ya wallafa a shafin Twitter cewa: "Me ka ce?"

A taron manema labarai kafin wasan hamayyar da za su yi da Manchester United - inda City za ta iya lashe Firimiyar bana idan ta yi nasara - an tambayi Guardiola kan rahotannin da ke cewa Raiola ya bayyana shi a matsayin "wawa" da kuma "kare" kan yadda ya ke mu'amala da mutane.

Guardiola ya ce: "Wata biyu da suka gabata ya tambaye ni ko zan sayi Pogba da Mkhitaryan. Don haka maganar kare... ya nuna rashin daraja kare."

Kocin ya ki bayyana cewa ko yana son Pogba sai dai ya ce dan wasan na Faransa mai shekara 25 "kwararre ne matuka".

Raiola na wakiltar manyan 'yan wasa da dama ciki har da tsohon dan wasan Sweden da kuma United Zlatan Ibrahimovic.