Man City na sa ran doke Man Utd ta dauki Premier

Pep Guardiola

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto,

Kociyan Manchester City Pep Guardiola ya ce kusan sun riga sun dauki kofin ma kawai, kuma 'yan wasansa sun cancanci dukkanin yabo

A ranar Asabar din nan ne za a yi karon-battar wasan hamayya a gasar Premier, inda jagora Manchester City za ta karbi bakuncin Manchester United a Etihad, kuma idan ta doke United din za ta dauki kofin.

Idan Man City wadda take ta daya a tebur da maki 84 a wasa 31 ta yi nasarar cin kofin Premier na bana, ya zama na uku ke nan da ta dauka a tarihinta, duk da sauran wasa shida bayan na yau din da ya rage a kammala gasar.

Ita kuwa babbar abokiyar hamayyar wato United ta biyu a teburin da maki 68, za ta so ta bata wa City wannan tarihi na zama kungiyar da za ta ci kofin da wuri bisa la'akari da ragowar wasannin da kwanaki da kuma wasannin da aka yi, sannan ta kara zama daram a matsayinta biyu.

Tuni Manchester City ta dauki kofin Carabao (EFL) na bana, amma kuma Wigan da ke karamar gasar League One ta yi waje da ita daga gasar cin kofin FA.

Sannan kuma a gasar cin kofin Zakarun Turai Liverpool ta doke da ta ci 3-0 a karawar farko ta wasansu na dab da na kusa da karshe a Anfield.

Sauran Wasannin Fafutukar Daukar Kofi a Turai:

Akwai wasu kungiyoyin da su ma suka yi fintinkau a sauran manyan gasar kasashen Turai hudu daga cikin biyar (Ingila da Faransa Da Jamus da Italiya da kuma Spaniya)

Yayin da ya rage wasa shida a kakar da ake wasanni 34, babbar tazarar da ake da ita, a Jamus ne, inda Bayern Munich take saman tebur a Bundesliga, kuma idan ta yi nasara Asabar din nan a gidan Augsburg za ta dauki kofin gasar na 28, kuma na shida a jere.

Bayern ce ta kafa tarihi na daukar kofin Bundesliga da wuri, a lokacin da ta ci kofin ranar 25 ga watan Maris a kakar 2013-14 karkashin Guardiola, da ragowar wasa bakwai.

A Faransa, Paris St-Germain ce ta daya da tazarar maki 17 a gaban masu rike da kofin Monaco, kuma PSG na bukatar maki biyar ne a wasa shida ta dauki kofi.

PSG ta dauki kofin a kakar 2015-16 ranar 13 ga watan Maris da ragowar wasa takwas, inda ta kammala kakar da maki 96 a wasa 38.

Barcelona ta kasance kungiyar da har yanzu ba a doke ba a manyan gasar kasashen Turai, kuma ta ba wa mai bi mata baya a La Liga Atletico Madrid ratar maki tara.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Har yanzu ba a doke Barcelona ba a bana a La Liga

A kakar 1960-61 da ta 1962-63, Real Madrid ta dauki kofin gasar da ragowar wasa biyar a lokacin gasar ta Spaniya mai kungiyoyi 16 ana fafatawa 30 ne a cikinta.

A Italiya nan ne fafatawar za ta fi zafi, domin kungiyar kociya Massimiliano Allegri wato Juventus ta ba wa Napoli ta biyu ratar maki hudu ne kawai, da ragowar wasa takwas.

Kungiyar ta kociya Maurizio Sarri, wato Napoli na harin daukar kofin na gasar Serie A a karon farko tun bayan tawagarta da Diego Maradona ya karfafa a kakar 1989-90.