Man Utd ta jinkirta wa Man City daukar kofi da ci 3-2

Paul Pogba (a dama) da Chris Smalling na murna Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Paul Pogba (a dama) da Chris Smalling su ne suka ci wa Manchester United kwallayenta uku a farfadowar da ta yi ta ban mamaki

Manchester City ta rasa damarta ta tabbatar mata cin kofin gasar Premier bana bayan da abokiyar hamayyarta Manchester United ta farfado ta doke ta 3-2 a Etihad.

Jagorar ta Premier wadda ke gida na bukatar ta doke abokiyar hamayyar tata ne a karawar ta dauki kofin, da ragowara wasa shida a kammala gasar.

Amma ta saryar da wannan dama bayan da ta yi sake United ta rama kwallo biyu da ta zura tun a kashin farko na wasan, bayan an shiga kashi na biyu.

Kyaftin din Man City Vincent Kompany ne ya fara daga raga a minti na 25, kafin kuma G√ľndogan ya kara ta biyu minti biyar tsakani.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a minti na 53 Paul Pogba ya rama wa Man United daya sannan bayan minti biyu ya farke ta biyun, kafin kuma Smalling ya ci ta uku a minti na 69.

Manchester City za ta kara a gidanta ranar Talata da Liverpool a wasa na biyu na matakin dab da na kusa da karshe na kofin Zakarun Turai.

Kafin ta je Wembley ta fafata da Tottenham a gasar ta Premier ranar Asabar.

Manchester United wadda a ranar Lahadi mai zuwa za ta karbi bakuncin ta karshe a tebur West Brom ta ci gaba da zama ta biyu da maki 71.

Gasar Jamus ta Bundesliga;

Kafin wasan na Ingila can a Jamus Bayern Munich sun sake daukar kofin gasar kasar ta Bundesliga bayan da suka lallasa Augsburg da ci 4-1.

Wannan shi ne karo na shida a jere da Bayern ke cin kofin na Bundesliga a jere.