Damben Shagon Musa da na Audu Mai Ramu

Damben Shagon Musa da na Audu Mai Ramu

Sama da dambatawa tara aka yi a safiyar Lahadi a gidan wasa na Ali Zuma da ke unguwar Dei-Dei a Abuja Nigeria.

Ciki har da karawar da aka tashi babu kisa tsakanin Shagon Bahagon Musan Kaduna daga Arewa da Shagon Audu Mai Ramu daga Guramada.

Mohammed Abdu ne ya hada rahoton

Wasan da aka yi kisa a ranar shi ne wanda Shagon Idi daga Guramada ya buge Shagon Dan Shariff daga Kudu a Turmin farko.

Sauran dambatawar canjaras aka yi:

Garkuwan Aleka daga Kudu da Dogon Washa Guramada

Shagon Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa da Shagon Dogon Kyallu Guramada

Ibrahim Na Mai Masauki Guramad da Dogon Aleka daga Kudu

Shagon Yalo Dan Suru Guramada da Dogon Bahagon Sisco daga Kudu

Dunan 'Yar Biyar Guramada da Shagon Autan Faya daga Kudu

Shagon Shagon Alhazai daga Arewa da Shagon Bahagon Dan Kanawa daga Kudu

Nokiyar Dogon Sani daga Arewa da Bahagon Garkuwan Cindo Guramada