'Yan wasan kulob din Panathinaikos sun fara yajin aiki

'Yan wasan Panathinaikos sun yi wasa filin Apostolos Nikolaids kuma sun ci kofin gasar frimiya ta Girka har sau 20 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan wasan Panathinaikos sun yi wasa filin Apostolos Nikolaids kuma sun ci kofin gasar frimiya ta Girka har sau 20

'Yan wasan kulob din Panathinaikos na kasar Girka sun fara yajin aiki saboda ba a biya su albashinsu na bara ba.

'Yan kwallon, wadanda suke jiran a biya su kudadensu na Disamba amma aka gaza yin hakan a 2018, sun fara yajin aikin ranar Litinin.

Sai dai kulob din ya shaida wa BBC cewa za a biya 'yan wasan kudadensu na watan Disamba ranar Alhamis kuma ana sa ran su dawo atisaye.

Ana sa ran wasan da za su kara na Super League da Atromitos zai gudana kamar yadda aka tsara.

Panathinaikos, wadanda suka lashe gasar Lig ta Girka sau 20, su ne na tara a teburin gasar ta bana.

A makon da ya gabata, an kwace musu maki uku saboda sun kasa biyan tsohon 'dan wasan baya na Jamus Jens Wemmer bashin da ya ke binsu.

Wannan shi ne lamari na baya-bayan nan da ya faru a gasar ta Super League.

A makon da ya gabata, an ci tarar 'yan wasan Olympiakos Yuro 400,000 sannan shugaban kulob din ya neme su da su tafi hutu saboda rashin taka rawar gani.

Hakazalika a watan da ya gabata, an dakatar da shugaban Paok Salonika na shekara uku bayan da ya shigo fili da bindiga a lokacin da suke kara wa da AEK Athens.

Labarai masu alaka