Kasa na 'girgiza' idan Messi ya ci kwallo

Messi Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Masu binciken sun ce kasa na girgiza idan Messi ya ci kwallo

Masana kimiyya a Spaniya sun gano cewa kasa na girgiza a birnin Barcelona idan dan wasan gaba na Argentina, Lionel Messi, ya ci wa kungiyarsa kwallo.

Masu binciken karkashin jagorancin Dr Jordi Diaz sun saka na'ura kusa da filin wasa na Camp Nou kuma tana daukar yadda kasa ta ke girgiza a duk lokacin da mutane suka yi farin ciki game da kwallon da Messi ya ci.

Sun ce karfin makin naurar na tashi idan magoya bayan kwallon kafa suka tashi suna tsalle suna shewa.

An dai saka naurar ne a cikin cibiyar da Dr Diaz ya ke aiki, wadda ta ke da nisan mita 500 da fiilin wasan Barcelona.

Da farko Dr Diaz ya aiwatar da shirin ne domin ya ja hankalin jama'a dangane da salon aikinsa na kimiyya.

Sai dai Dr Diaz da sauran ma'aikatansa sun lura da cewa akwai wasu abubuwa da ke faruwa, abin da ya sa suka karfafa binciken da suke yi.

Hakkin mallakar hoto ICTJA-CSIC
Image caption Filin wasan ya kaure da ihu a lokacin da kwallo ta shiga raga a karo na shida

Bayan binciken da suke yi kan wasannin Barcelona, masu binciken daga cibiyar kimiyya ta Jaume Almera da ke Barcelona na kuma bibiyar yadda kasa ta ke girgiza idan motoci sun wuce da kuma yadda hakan ya ke shafar gine-ginen da ke wurin.

Sun kuma ce haka al'amarin yake a tashar jiragen kasa.

"Ya soma ne kamar wani abu na almara, amma yanzu sun fara binciken kimiyya akansa", kamar yadda Dr Diaz ya shaida wa BBC.

ya kara da cewa "daya na da nasaba da aikin injiniya, sannin yadda hanyoyi da gine-gine suke girgiza sakamakon zirga-zirgar da mutane su ke yi zuwa wurare daban-daban. Yanzu mun tuntubi makarantun da ke koyar da aikin injiniya game da gaskiyar alamarin."

Labarai masu alaka