Liverpool ta lallasa Manchester City

Mohamed Salah Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Mohamed Salah na da hannu a kwallo 50 a bana - ya ci 39 sannan ya sa aka ci 11

Liverpool ta kai zagayen dab da na karshe a gasar cin kofin zakarun Turai a karon farko cikin shekara 10 bayan da ta doke Manchester City da 2-1 wato 5-1 jumulla bayan wasa biyu.

City ce ta fara zura kwallo ta hannun Gabriel Jesus bayan sakan 116 bayan da Raheem Sterling ya ba shi kwallo.

Bernardo Silva ya daki turke kafin Sane ya ci kwallo amma aka hana saboda zargin satar gida duk da cewa James Milner ne ya taba kwallon.

Mohamed Salah ne ya rama wa Liverpool kafin Roberto Firmino ya ci ta biyu.

Liverpool za ta san kulob din da za ta kara da shi a ranar Juma'a lokacin da za a raba kungiyoyin a Nyon, na kasar Switzerland.

City ce ta mamaye kashin farko na wasan inda ta zubar da damarmaki, kafin Liverpool ta farfado a zagaye na biyu.

Alkalin wasa ya kora Pep Guardiola cikin 'yan kallo bayan da ya yi korafi kan hana kwallon da Sani ya ci a lokacin da aka ta fi hutun rabin lokaci.

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba