Zakarun Turai: Ana tuhumar Guardiola da Liverpool

Manchester City boss Pep Guardiola Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An kora Guardiola cikin 'yan kallo bayan da ya yi korafi ga alkalin wasa

Hukumar Kwallon Kafa ta Turai (Uefa) ta tuhumi kocin Manchester City Pep Guardiola da nuna rashin da'a a wasan da Liverpool ta doke su a gasar zakarun Turai ranar Talata.

Uefa ta kuma tuhumi Liverpool kan yadda magoya bayanta suka rinka wasan tartsatsin wuta da kuma jefa kwalabe cikin filin wasa na Etihad.

An kora Guardiola cikin 'yan kallo bayan da ya yi korafi kan kwallon da Sane ya zura wacce alkali wasa Antonio Mateu Lahoz ya hana.

Za a saurari tuhumar da aka yi musu a ranar 31 ga wata Mayu.

Laifin Guardiola shi ne na yin magana da tawagar City bayan an kore shi.

Da ma dai Liverpool na fuskantar tuhuma kan wasan tartsatsin wuta da jefa kwalabe, da kuma yin barna bayan da aka kai wa motar 'yan wasan City hari a Anfield lokacin da suka yi wasan farko.