Gabana ya fadi kafin na buga fanareti - Ronaldo

Ronaldo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Cristiano Ronaldo ya ci kwallaye 41 a kakar bana

Cristiano Ronaldo ya ce sai da ya kwantar da hankalinsa sosai kafin ya buga fanaretin da ya ci ana daf da tashi daga wasansu da Juventus.

Fanaretin da Ronaldo ya ci ne ya taimakawa Real Madrid kai wa zagayen daf da na karshe a gasar zakarun Turai.

"Faduwar gaba na ta karu, amma na kwantar da hankali, domin na san ni zan yanke hukunci," a cewar Ronaldo.

Real Madrid ta samu fanareti ne a mintin karshe a Bernerbeu a yayin da Juventus ta rama kwallo ukun da ta zura ma ta a karawa ta farko a Italiya.

Ronaldo ya ce bai taba tunanin ba za su yi nasara ba a wasan.

Dan wasan na Portugal ya ci kwallo 41 a kakar bana, kuma wasa 11 ke nan a jere yana cin kwallo a raga.

A ranar Juma'a ne Real Madrid za ta san kungiyar da za ta hadu da ita a zagayen daf da na karshe tsakanin Roma da Liverpool da kuma Bayern Munich.

Labarai masu alaka