Kofin Europa: Arsenal ta kai gaba da kyar

Danny Welbeck na murnar farke kwallon farko Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Arsenal ta tsira a Moscow da canjaras 2-2, bayan da a wasan farko ta lallasa CSKA 4-1

Arsenal ta yi nasarar zuwa wasan kusa da na karshe na gasar cin Kofin Turai na Europa bayan da ta yi 2-2 a gidan CSKA Moscow, jumulla 6-3 gida da waje.

Gunners din sun shiga tsananin damuwa ganin cewa an fara zura musu kwallo biyu a wasan na Alhamis, ta hannun Chalov a minti 39 da kuma Nababkin a minti na 50, wanda da ba su farke ba da sun yi muguwar rawa irin ta Barcelona.

Ita dai Barcelona ta gamu da gamonta a hannun Roma ranar Talata, bayan da kungiyar ta Italiya ta kawar da nasarar da Barcelona ta yi a karawarsu ta farko da ci 4-1, ta kai wasan kusa da karshe na gasar ta Zakarun Turai ta Uefa.

Arsenal ta tsallake rijiya da baya bayan da Welbeck ya ci mata a minti na 75, sannan kuma Ramsey ya farke ta biyun bayan cikar minti 90 na wasan, aka tashi 2-2.

Kungiyar za ta hadu da Atletico Madrid ko Marseille kuma Red Bull Salzburg, wanda kuma idan har ta kai wasan karshe ta dauki kofin za ta samu gurbin wasan Kofin Zakarun Turai na Uefa na gaba, abin da kusan ta rasa a gasar Premier.

Za a fara fitar da jadawalin Kofin na Europa da karfe 11:00 na rana agogon Najeriya sannan kuma da karfe 12:00 na rana agogon Najeriyar a fitar da jadawalin wasan dab da na karshe na Kofin Turai na Uefa.

Da wacce kungiya Liverpool za ta kara?

Wannan shi ne karon farko a cikin shekara tara da kungiyar ta Arsene Wenger ta kai wasan dab da na karshe na gasar Turai.

Kociyan ya shigo da 'yan wasa bakwai da ba sa cikin wadanda ya yi nasarar doke Southampton da su 3-2 a gasar Premier ranar Lahadi, wadanda daman ya yi tanadi domin karawar ta Europa.

A karawar ta Moscow ya fara da manyan 'yan wasansa da ya ajiye kamar su Mesut Ozil da Ramsey da kuma Wilshere.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Liverpool na harin daukar Kofin Turai na shida, inda za ta kasance ta uku da yawan kofin bayan Real Madrid, mai 12 da AC Milan mai bakwai

Kungiyar ta Arsenal, wadda ta rasa Jack Wilshere saboda raunin da ya ji a wasan za ta kasance cikin kungiyoyi hudu wadanda za a fitar da jadawalin wasan dab da na karshe da su na gasar ta Kofin Europa, ranar Juma'a a birnin Nyon, na Switzerland.

Liverpool za ta san abokiyar karawarta a ranar Juma'ar nan a jadawalin wasan dab da na karshe da za a fitar na gasar Kofin Turai na Uefa a birnin Nyon na Switzerland da karfe 12:00 na rana agogon Najeriya.

Kungiyar wadda ta yi waje da Manchester City a wasan dab da na kusa da karshe za ta hadu da Bayern Munich ko Real Madrid ko kuma Roma.