Arsenal za ta hadu da Atletico Madrid a gasar Europa

Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images

Arsenal za ta kara da Atletico Madrid a wasan kusa da na karshe a gasar Europa, yayin da RB Salzburg za ta hadu da Marseille.

Arsenal za ta fara wasan farko ne a gida a ranar Alhamis 26 ga watan Afrilu, sai kuma ta je gidan Atletico a ranar 3 ga watan Mayu.

Za a yi wasan karshe na gasar ne a ranar 16 ga watan Mayu a birnin Lyon na kasar Faransa, inda duk kungiyar da ta lashe kofin za ta samu gurbin zuwa Gasar Zakarun Turai na badi.

Arsenal ta samu nasarar kai wa ga matakin wasan kusa da na karshe ne bayan ta doke CSKA Moscow da jumullar kwallo 6-3.

Labarai masu alaka