Maki uku ya rage Man City ta dauki Premier bayan doke Tottenham 3-1

Fanaretin da Ilkay Gundogan ya ci Tottenham Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Manchester City na bukatar maki uku ne kawai a sauran wasanninta biyar ta dauki kofin

Manchester City na dab da daukar kofin Premier bayan da ta farfado daga fitar da ita daga gasar Zakarun Turai, ta doke Tottenham 3-1 a Wembley.

Kungiyar ta Pep Guardiola na bukatar maki uku ne kawai ta ci kofin na Premier, amma kuma za ta iya daukansa idan Manchester United ta biyu ta sha kashi a hannun West Brom ranar Lahadi ko kuma a hannun Bournemouth ranar Laraba.

Amma indai ba haka ba to 'yan wasan na City za su zama zakarun gasar na bana idan kawai suka yi nasara a karawarsu ta gaba da Swansea ranar 22 ga watan nan na Afrilu.

Wasan ya karfafa wa City guiwa bayan takaicin da suka gamu da shi ranar Talata, inda Liverpool ta yi waje da su daga gasar Zakarun Turai a wasan dab da na kusa da karshe da ci 5-1 a karawa biyu.

Gabriel Jesus ne ya fara ci wa City kwallo a minti na 22, minti uku tsakani kuma sai golan Tottenham kuma na Faransa ya jawo fanareti bayan da ya yi wa Raheem Sterling keta, ko da yake daga baya hoton bidiyo ya nuna cewa ba a cikin da'irar gidansa ya yi ketar ba.

Ilkay Gundogan ne ya buga fanaretin inda ya ci wa Man City bal ta biyu, amma Tottenham ta farke daya a minti na 42 ta hannun Eriksen, kafin kuma Sterling ya ci ta karshe wato ta uku a minti na 72, bal din da ta dan kwantar da hankalin 'yan City.

Rashin nasarar shi ne na farko da Tottenham ta gamu da shi a gasar ta Premier tun bayan da ta sha kashi 4-1 a gidan City din ranar 16 ga watan Disamba, kuma ya kawo karshen bajintarta ta wasa 14 ba tare da an doke kungiyar ba.

Kungiyar ta Mauricio Pochettino ta ci gaba da zama ta hudu a tebur, da tazarar maki shida tsakaninta da Chelsea ta biyar.

Sakamakon Sauran Wasannin Premier na Asabar:

Southampton 2-3 Chelsea

Burnley 2-1 Leicester

Crystal Palace 3-2 Brighton

Huddersfield 1-0 Watford

SWansea 1-1 Everton

Liverpool 3-0 Bournemouth