Mohamed Salah ya kawar da bajintar Didier Drogba

Bal din da Mohamed Salah ya ci ta 40 a wasa 45 da ya yi wa Liverpool a kakar nan Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bal din ta 40 da ya ci a wasa na 45 a Liverpool a kakar nan, ta sa kungiyar doke Bournemouth 3-0

Mohamed Salah ya kawar da tarihin da Didier Drogba ya kafa a gasar Premier na kasancewa dan wasan Afirka da ya fi cin kwallo a kaka daya, bayan da ya zura daya daga cin kwallo uku da Liverpool ta doke Bournemouth.

Drogba ya yi bajintar cin kwallo 29 a kaka daya a gasar ta Premier, to amma kuma bal din da Salah ya ci a karawar ta Asabar ta zama ta 30 da ya ci a kakar nan, abin da ya sa ya wuce tsohon dan wasan na Chelsea wanda ya yi tasa bajintar a kakar 2009/10.

Nasarar ta sa Liverpool ta ci gaba da zama a matsayi na uku a tebur amma yanzu maki daya ne kawai tsakaninta da ta biyu Manchester United.

Masu masaukin bakin sun fara wasan da kyau inda Sadio Mane ya fara daga raga minti bakwai da shiga fili.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne a minti na 69 Salah ya ci ta biyu, wadda ta ba shi damar zama na daya a 'yan wasan Afirka da suka fi cin kwallo a kaka dayar a Premier, kuma ta 40 da ya ci wa kungiyar a dukkanin gasa a kakar nan.

Bal din ta sa ya zama na farko da ya yi wannan bajinta a Liverpool tun bayan Ian Rush a kakar 1986-87. Inda shi ma ya ci wa kungiyar kwallo 40 a kaka daya.

Roberto Firmino ne ya ci wa kungiyar bal ta uku, wadda ta kasance ta 15 da ya ci a Premier a bana, kuma ta tabbatar da nasara ta biyar da kungiyar ke yi a jere a wasa shida.

Kociyan Liverpool Jurgen Klopp wanda ya ce yawan kwallon da suke ci a bana abin kamar hauka, ya ce duk wani korafi da ake yi a kan Salah da suka sayo daga Roma a bazarar da ta wuce a kan fam miliyan 34 a yanzu ya kau.

Labarai masu alaka