Matar alkalin wasa Micheal Oliver na fuskantar barazana

Michael Oliver lokacin da ya ba wa Gianluigi Buffon jan kati (na kora) Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Michael Oliver ya kori mai tsaron raga Gianluigi Buffon daga wasan saboda ya yi korafi kan ba wa Real Madrid fanareti ana dab da tashi

'Yan sanda a Ingila suna gudanar da bicike kan sakonnin waya na barazana da cin zarafi da ake aika wa matar lafirin gasar Premier wanda ya yi alkalancin wasan kofin Zakarun Turai tsakanin Real Madrid da Juventus Michael Oliver.

Oliver ya ba wa Real Madrid fanareti ana dab da tashi daga wasan, abin da ya ba ta damar fitar da Juventus daga gasar ranar Laraba.

Hukuncin ya sa mai tsaron ragar Juventus kuma kyaftin Gianluigi Buffon ya soki alkalin wasan, lamarin da ya sa ya kori golan a lokacin.

Haka kuma wasu kafafen watsa labarai na kasar Italiya su ma sun yi ta suka ga alkalin wasan.

BBC ta fahimci cewa an sanya lambar wayar matar Oliver mai suna Lucy wadda take alkalancin wasa a babbar gasar kwallon kafa ta mata ta Ingila, (Women's Super League), wadda kuma take alkalancin a wasannin maza wadanda ba na gasar lig ba, a shafukan sada zumunta da muhawara (zumhawara), bayan wasan na Real Madrid da Juventus, abin da ya sa aka yi ta aika mata da sakonnin zagi.

Kungiyar manyan alkalan wasa, PGMOL, ta ce tana bayar da goyon bayanta ga lafirin da matarsa, ta kuma yi alla-wadai da cin zarafin da ake wa Lucy a shafukan sada zumunta da muhawara (zumhawara).

A wasan na Bernabeu a Madrid alkalin wasa Oliver ya kori kyaftin din Juventus kuma mai tsaron raga Buffon saboda sukar da ya yi masa a kan fanaretin da ya bayar a minti na 93.

Bayan wasan ya gaya wa manema labarai cewa alkalin wasan dan Ingila yana da jakar shara ne a matsayin zuciya; ma'ana ba shi da kan gado, bai san abin da yake yi ba, sakarai ne.

A ranar Asabar Buffon ya ce yana nan a kan bakansa na wadannan kalamai da ya yi gaba daya.

Golan mai shekara 40 ya yarda cewa wasu daga cikin kalmomin da ya yi amfani da su, sun yi tsauri, amma duk da haka ya ce lafirin mai shekara 33 ya yi kankanta a ce ya yi alkalancin wasa mai wannan muhimmanci.

A wata hira da gidan talabijin na Italiya, Buffon ya ce: ''Dole ne na kare abokan wasana da magoya bayan kungiyarmu, ko da ta cikin fushi ne. Dole ne na yi haka, ko da kuwa hakan zai bata min suna.''

Haka kuma 'yan sanda na gudanar da bincike a kan rahotannin da ke cewa wasu mutanen ma suna zuwa suna buga kofar gidan lafirin da matar tasa, suna kwarara musu zagi ta akwatin sanya wasikarsu.

Yanzu dai 'yan sanda sun tsayar da lambar wayar matar, ko da yake wasu magoya bayan wasan kwallon kafar suna zagin da cin mutunci ta shafukanta na sada zumunta da muhawara (zumhawara).