Manchester City ta dauki kofin Premier ta Ingila

Manchester City
Image caption Wannan ne karon farko da Pep Guardiola ya lashe gasar Premier

A fagen kwallon kafa, kulob din Manchester City ya lashe kofin gasar Premier ta nan Ingila, duk da cewa kulob din bai buga wasa a ranar Lahadin nan ba.

Babbar abokiyar hamayyarsu Machester United, ta sha kashi a gida a hannun kulob din da ke kasan teburin gasar, West Brom da ci 1-0.

Hakan na nufin ba za su taba iya kamo Manchester City a yawan maki ba.

Wannan ne karon farko da kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya lashe kofin gasar ta Premier.

Kulob din na Manchester City ya na da sauran wasanni biyar a gaba.