Real Madrid ta zama ta uku bayan doke Malaga 2-1

Isco lokacin da yake cin Malaga Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kusan Isco ya tausaya da bayar da hakuri ga magoya bayan tsohuwar kungiyarsa Malaga lokacin da ya ci su. Kungiyar da ya yi kaka biyu kafin ya koma Real a 2013

Real Madrid ta koma ta uku a teburin La Liga da maki 67 bayan da ta bi ta karshe Malaga har gida ta doke ta da ci 2-1.

A wasan na Lahadi Real ta ajiye da dama daga cikin manyan 'yan wasanta na yau da kullum da suka hada da Cristiano Ronaldo da Gareth Bale, bayan tsallake rijiya da baya da ta yi a gasar Zakarun Turai a hannun Juventus da ci 4-3 jumulla.

Isco ya fara ci a minti na 29 inda ya zura kwallo a ragar tsohuwar kungiyar tasa, da wani kyakkyawan bugun-tazara.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne kuma a minti na 69 Isco din ya ba wa Casemiro bal din da ya zura ta biyu.

Ana dab da tashi bayan minti 90 na ka'ida Diego Rolan ya ci wa Malaga dayar bayan kukuren da Jesus Vallejo ya tafka.

Masu masaukin bakin wadanda wasan La Liga hudu kawai suka ci a bana, maki 14 ne tsakaninsu da tsira daga gasar yayin da ya rage wasa shida a kammala.

Real kuwa wadda ta wuce saman Valencia a tebur da wannan nasara, maki hudu ne tsakaninta da ta biyu Atletico Madrid, wadda ita kuma ta doke Levante 3-0 a ranar Lahadin.

Wasan Atletico Madrid da Levante

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Fernando Torres ya ci wa Atletico bal takwas a kakar nan, uku daga ciki a La Liga

Fernando Torres ya ci bal dinsa ta 100 a La Liga a wasan da Atletico ta doke Levante 3-0, a makon da aka sanar dan wasan zai bar kungiyar a bazaran nan.

Tsohon dan wasan na Liverpool da Chelsea mai shekara 34, wanda ba safai ake sa shi akai akai a kungiyar ba a bana, ya maye gurbin Antoine Griezmann ne a wasan inda ya ci wa Atletico bal ta uku a minti 77.

Angel Correa ne ya fara ci musu a minti na 33, yayin da shi kuma Griezmann ya ci ta biyu a minti na 48.

Atletico wadda za ta yi wasan kusa da karshe na kofin Turai na Europa da Arsenal ranar 26 ga watan Afrilu da kuma 3 ga watan Mayu, ta ci gaba da zama ta biyu a teburin La Liga da maki 11 tsakaninta da Barcelona.

Kungiyar ta ci wasanta10 na gida na karshen nan a gasar ta Spaniya, inda sau daya kawai aka zura mata kwallo a raga.

Sakamakon sauran wasannin na La Liga na Lahadi

Eibar 0- 1 Alav├ęs

Getafe 1-0 Espanyol

Labarai masu alaka