Kalli 'yan wasan da suka fitar da Manchester City kunya

A ranar Lahadi ne Manchester City ta lashe kofin Premier bayan Manchester United ta sha kashi a gidanta a hannun West Bromwich Albion.

City ta zama zakara a Ingila ne da tazarar maki 16 tsakaninta da Manchester United da ke matsayi na biyu.

Kofin Premier na uku ke nan da City ta lashe a shekara bakwai, kuma na biyar a tarihin kungiyar.

Manchester City ta lashe kofin ne ana saura wasa biyar a kammala gasar, tarihin da Manchester United ta taba kafawa a kakar 2000-01.

Idan kuma City ta samu maki tara daga sauran wasa biyar da ya rage, zai kasance ta samu maki 95, tarihin da Chelsea ta kafa a kakar 2004-05.

BBC ta yi nazari kan 'yan wasan da suka fi taka rawa ga samun nasarar Manchester City a bana.

Kevin De Bruyne

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Pep Guardiola ya ce De Bruyne ne ya taimaka wa City zama "gagara gasa."

Ana ganin Kevin De Bruyne na iya lashe kyautar gwarzon dan wasan Premier na bana, duk da yana hamayya da Mohammed Salah na Liverpool.

De Bruyne ne ya fi yawan taimakawa a ci kwallo a gasar ta bana.

Amma rawar da dan wasan na Belgium yake takawa a Manchester City ta zarce haka, kamar yadda wasu ke kiran shi "zuciyar Manchester City."

A lokacin da yake yabonsa, kocinsa Pep Guardiola ya ce De Bruyne ne ya taimaka wa City zama "gagara gasa."

David Silva

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Silva ya dade yana nuna bajinta a City

Samun De Bruyne da David Silva a tsakiyar fili ya kara wa Manchester City karfi tsakaninta da abokan hamayya.

David Silva na cikin 'yan wasan da ke nuna kansu a manyan wasannin Manchester City.

Silva ne ya fara bude raga a karawar hamayya da Manchester United a Old Trafford.

A kakar bana Silva ya taimaka an ci kwallo 11 a Premier, kuma shi ne na uku a jerin 'yan wasan da suka fi bada kwallo a ci.

Raheem Sterling

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wannan ce kaka mafi kyau ga matashin dan kwallon a tahirin rayuwarsa

Raheem Sterling bai taba nuna kwazo ba kamar kakar bana.

Wasu na ganin Guardiola ne ya sauya dan wasan na Ingila mai shekaru 24.

Sterling ne dan wasan City na biyu da ya fi yawan cin kwallaye a raga bayan Sergio Aguero, kuma kwallayensa na cikin wadanda suka yi tasiri ga nasarar lashe kofin Premier.

Raheem Sterling ya ci kwallo biyu a kwanaki uku ana dab da tashi wasannin da Manchester City ta doke Huddersfield da Southampton 2-1 a watan Nuwamba.

Sergio Aguero

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sergio Aguero ya zama abin da Hausawa ke cewa "a dade ana yi sai gaskiya"

Sergio Aguero ya yi zamani da 'yan wasa da kuma masu horar da 'yan wasa da dama a zamanin da Manchester City ta fara tashe.

Amma duk da haka dan wasan ya ci gaba da zama dodon raga a kulub din.

Dan wasan na Argentina da ya koma City a 2011, kuma yanzu shi ne wanda ya fi yawan cin kwallaye a tarihin kungiyar.

A bana ma Sergio Aguero ne kan gaba da yawan cin kwallaye inda ya ci wa Manchester City kwallo 21.

Dan wasan ya kafa tarihi a bana duk da ya fuskanci kalubale bayan zuwan Gabriel Jesus da Guardiola ya sayo a watan Janairu.

Ederson Santana de Moraes

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption City ta kafa wani sabon Tarihi a Premier inda ta buga wasa 18 tana yin nasara a jere

Ederson golan da Manchester City ta sayo a kan fam miliyan 35 ana dab da kammala kakar da ta gabata, yana cikin 'yan wasan da suka taka muhimmiyar rawa.

Golan ya saje da irin salon kwallon da Guardiola yake so, inda ya kwace gurbin Claudio Bravo.

Guardiola ya fi son ana taba kwallo da gola, kuma Ederson ya iya take kwallo da yanka.

Sannan yana taimakawa 'yan wasan gaba da doguwar kwallo domin kai farmaki ga abokan hamayya, tsarin da Guardiola ya fi so.

Pep Guardiola

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Pep Guardiola ya burge masu sharhi da sha'awar kwallon kafa da dama saboda yadda City ke murza-leda

Guardiola ya lashe kofin Premier ne a kakarsa ta biyu a Manchester City.

Ana ganin cefanen sabbin 'yan wasa da Guardiola ya yi sun taimaka ma sa, musamman Gabriel Jesus da Leroy Sane da John Stones da Benjamin Mendy da Bernardo Silva da kuma Ederson.

Kuma salon tsarin kwallon tsohon kocin na Barcelona da Bayern Munich shi ne ya yi tasiri a Manchester City.

Labarai masu alaka