Da gaske ne Mo Salah zai koma Real Madrid?

Mo Salah Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An fara rade-radi kan makomar Mo Salah

Rahotanni a Spaniya na nuna cewa Real Madrid za ta yi kokarin sayen dan wasan Liverpool Mohammed Salah a kokarin da suke yi na taka wa barcelona birki a badi.

Jaridar Express ta rawaito cewa Madrid na shirin yin tankade da rairaya a 'yan wasanta bayan mummunar rawar da suka taka a bana.

Wasu kafafen yada labarai na cewa kocin Madrid Zidane ya shaida wa shugaban kulob din cewa yana sha'awar a sayo masa dan kwallon na Liverpool.

Dan wasan na Masar ya koma Liverpool daga Roma a kan kudi fan miliyan 37.

Sai dai ana ganin darajarsa ta karu saboda rawar da ya taka tun komawarsa Liverpool.

Wasu na ganin ya kara kusan dala miliyan 100 a kan farashinsa na asali.

Dan wasan ya zura kwallo 40 a kakar bana, inda ya jagoranci Liverpool ta kai wasan dab da na karshe a gasar Zakarun Turai a karon farko cikin shekara 11.

Kuma jaridar Diario Gol ta ce Zidane ya shaida wa Perez cewa yana son dan kwallon ya jagoranci 'yan wasan gaban kulob din a badi.

Sai dai ana ganin duk da wannan matsayin Liverpool ba za ta sauya ba game da dan wasan.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mo Salah ya zura kwallo 40 a kakar bana a Liverpool
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kocin Real Madrid Zidane na fuskantar matsin lamba saboda rashin taka rawar gani a bana

Labarai masu alaka