Kalli hotunan 'yan wasan Madrid da za su fafata da Athletic

'Yan wasan Real Madrid Hakkin mallakar hoto Real Madrid
Image caption Real Madrid za ta nemi karbe matsayi na biyu a teburin La liga idan ta samu maki uku a wasanta da Athletic Bilbao a Santiago Bernabeu

'Yan wasan Real Madrid na ci gaba da yin horo a shirn da suke yi na kece raini da kungiyar Athletic Club a ranar Laraba a gasar La Liga.

Mun zabo muku wasu daga cikin hotunan 'yan wasan da za su fafata a wannan wasa a lokacin da suke atisaye:

Hakkin mallakar hoto Real Madrid
Image caption Cristiano Ronaldo da ke kan ganiyarsa a yanzu, ana sa ran shi zai jagoranci tawagar 'yan wasan gaba na Madrid bayan Zidane ya ajiye shi a wasansu da Malaga
Hakkin mallakar hoto Real Madrid
Image caption Sau uku akwai aka doke Real Madrid a dukkanin wasanni 15 da ta buga a gidanta a jere a bana
Hakkin mallakar hoto Real Madrid
Image caption Real Madrid ta ci akalla kwallo biyu a ragar Athletic Bilabo a haduwa 13 da suka yi a baya
Hakkin mallakar hoto Real Madrid
Image caption Ana hasashen Zidane zai sake ajiye wasu manyan 'yan wasansa domin gasar zakarun Turai da Bayern Munich
Hakkin mallakar hoto Real Madrid
Image caption Idan Madrid ta samu nasara a karawarta da Bilbao, zai kasance maki daya tsakaninta da Atletico Madrid da ke matsayi na biyu a La Liga
Hakkin mallakar hoto Real Madrid
Image caption Ana sa ran Zidane zai ajiye Nacho saboda bai gama murmurewa ba daga raunin da ya samu a wasansu da Las Palmas
Hakkin mallakar hoto Real Madrid
Image caption Ronaldo shi ne na biyu da yawan cin kwallaye a raga a La liga inda ya ci 23.

Labarai masu alaka