Alex Ferguson ya jinjinawa Wenger

Sir Alex Ferguson da Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ferguson da Wenger sun shafe shekaru suna hamayya a lokutan da kungiyoyinsu suka mamaye gasar Premier na tsawon shekaru.

Tsohon kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya jinjinawa kocin Arsenal mai barin gado Arsene Wenger.

A ranar Juma'a ne kocin dan kasar Faransa ya bayyana cewa zai bar Gunners a karshen kakar bana.

Wannan na nufin zai tafi shekara guda kafin kwantiraginsa ta kare.

Ferguson ya ce Wenger na "daya daga cikin kociyoyi mafiya kwarewa a tarihin gasar Premier".

Ya kara da jinjinawa "basirarsa, da kwazonsa da kuma jajircewarsa".

Ferguson da Wenger sun shafe shekaru suna hamayya a lokutan da kungiyoyinsu suka mamaye gasar Premier na tsawon shekaru.

Wenger ya lashe gasar Pemier uku da kuma kofin FA bakwai - wanda babu wanda ya kaishi lashe kofin na FA.

A nasa bangaren Ferguson ya lashe gasar Lig sau 13 a shekara 26 da ya shafe a Manchester United kafin ya yi ritaya a 2013.

Henry na daya daga cikin wadanda ake hasashen za su iya maye gurbin Wenger.

A yanzu shi ne mataimakin koci na biyu a tawagar kwallon kafa ta kasar Belgium.

Tsohon dan wasan Arsenal Thierry Henry ya ce Wenger ya bar "tarihin da ba za a iya gogewa ba".

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ferguson ya ce Wenger na "daya daga cikin kociyoyi mafiya kwarewa a tarihin gasar Premier".