'Mo Salah ya zama abin kwaikwayo ga 'ya'yan Musulmi'

Rabiya Limbada da 'ya'yanta Hakkin mallakar hoto Rabiya Limbada
Image caption Rabiya Limbada ta ce Mo Salah ya zama abin misali ga 'ya'yanta Muhammad da Hanaa

Mohamed Salah! Dan wasan kwallon kafa da ya zama abin kwaikwayo ga yara kuma tauraron kasar Masar da ke hada kan al'umma.

Wata uwa Musulma Rabiya Limbada ta bayyana yadda dan wasan Liverpool, Mo Salah, ya yi tasiri ga rayuwar 'ya'yanta saboda yadda yake kamanni da su a matsayinsa na Musulmi.

Ta ce: ""Gidana ya rude da ihu a yayin da Mohamed Salah ya fara zura kwallo a ragar Roma a gasar zakarun Turai a daren Talata.

'Ya'yana Hanaa, mai shekara takwas da Muhammad mai shekara shida sun ruda gida da murna a yayin da muke kallon lokacin da Salah ya kai goshinsa kasa, kamar yadda ya saba idan ya ci kwallo.

Yana da wahala a samu gidan da ba a damu da martabar dan wasan na Liverpool ba a sassan Ingila, ko ma duniya baki daya.

Yadda yake kan ganiyarsa, Mohamed Salah yana hada kan al'umma.

Yana Addu'a a fili

Yana addu'a a fili, sannan ya yi wasa da gemunsa, kuma yadda yake taka leda ya kayatar da mutane a bana.

Ko kun san girman yadda wannan ya yi tasiri ga 'ya'ya kamar nawa? Ya zama abin misali a zamaninmu.

A gabashin Landan aka haife ni kuma na girma, iyayena sun yi hijira zuwa Ingila daga Yemen da Burma.

Ba kamar sauran mutane da muke shekaru daya da su ba, ban taba damuwa da ra'ayin kasancewa a matsayin 'yar kasa ba.

Duk da haka, ina da masaniyar cewa yara a zamanin nan daga addinai daban-daban tunaninsu ya bambanta.

Tasirin labaran duniya da suke saurare kan iya zama dalilin da zai sa su yin taka-tsan-tsan wajen nuna addininsu.

Don haka ba abin mamaki ba ne idan dan wasa kamar Salah ya ratsa zukatansu.

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Mo Salah ne dan wasan Masar na farko da ya karbi kyautar gwarzon dan wasan Ingila

'Yata Hanaa tana jin dadi a lokacin da take kallon Salah ya daga hannayensa sama yana addu'a bayan ya ci kwallo.

"Mama, mu ma muna yin haka!" in ji ta.

Kamar al'adar Musulmi, yawancin maza suna barin gemu, kuma haka ma Salah.

A lokacin da na kama yarona mai shekara shida a tsaye gaban madubi yana kokarin jan gashinsa na yara a gemunsa, tare da ikirarin wai yana da gashin gemu kamar Salah, sai da na ji wani abu a zuciyata.

Ko shakka babu shi ne dan wasan da ya fi kowa a duniya a yanzu.

Mohamed Salah yana hada kan al'umma, kuma ni ina cikin wadanda suka tabbatar da haka.

Salah Sarki ne

An ta nuna magoya bayan Liverpool a Anfield rike da hoton Salah an rubuta Sarkin Masar.

Wasu magoya bayan Liverpool sun yi ta rera waka a kan masallaci da Musulmi a Ingila saboda kaunar Salah, al'amarin da ya burge Musulmi a sassan duniya.

A kasarsa Masar, Salah Sarki ne.

Salah ne ya taimaka wa Masar samun gurbi a gasar cin kofin duniya a Rasha dalilin kwallon da ya ci a fanareti.

Ko yana buga wa Liverpool ko Masar wasa, a cikin minti 90 na kwallo yana hada kan al'ummar kasarsa inda ake yin watsi da duk wani bambanci na siyasa domin kallon tauraron kasar.

Hakkin mallakar hoto Rabiya Limbada
Image caption Hanaa da Muhammad, masoyan Mo Salah

Salah ya sauya ra'ayin wasu game da musulumai

Mohamed Salah yana canza yadda wasu suke kallon musulmai, kuma wannan wani abu ne sabo. A karon farko, musulmi bai koma wani abin tsoro ba.

Yawancin abokaina da muke goyon bayan Liverpool sun shaida min cewa halayensa da dabi'unsa abin yabawa ne kuma sun kalubalanci ra'ayoyin ma su karamin tunani.

Zan iya cewa abin da na sani a yanzu shi ne Mohamed Salah ya yi kokari sosai wajen hada kan mabiya mabambanta addinai a cikin kankanin lokacinsa a Liverpool.

Wanene Mo Salah?

-Cikakken suna: Mohamed Salah Ghal

-Ranar Haihuwa: 15/06/1992

-Garin Haihuwa: El Gharbia, Masar

-Kulub: Liverpool FC - daga AS Roma ya zo a kan fam miliyan 34 a watan Yunin 2017

-Kasarsa: Masar

- Dan wasan Masar na farko da ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Ingila a Premier.

A wata hira da aka yi da shi kwanan nan, kocin Liverpool Jurgen Klopp ya yi bayani game da yadda Salah da sauran 'yan wasansa Musulmi Sadio Mane da Emre Can suke yin alwala a matsayin shiri kafin shiga filin wasa.

Klopp ya ce sauran 'yan wasansa suna jiransu su idar sannan suna girmama lokacin da suke bukata.

Rabiya Limbada ta ce yana da wahala ta iya takaita muhimmacin kalaman Klopp ga 'ya'yanta.

Sai mun yi alwala kafin mu yi salloli biyar da muke yi a rana. Alwala tsari ne na tsarkake jiki domin tsayuwa a gaban Allah.

Hakkin mallakar hoto Rabiya Limbada
Image caption Rabiya Limbada tare da mijinta Imran da 'ya'yansu Hanaa da Muhammad

Ga irin wannan dan karamin aikin da har aka bayyana tare da girmamawa, babban sako ne ga 'ya'yana da kuma wasu kamarsu a fadin duniya.

Addinin Musulunci ya yi magana sosai game da girmamawa da kuma jajircewa.

Kuma wannan shi ne kashin bayan tarbiyar iyaye ga 'ya'yansu domin zama mutane na gari.

A kan haka ne mijina a kullum yake ba da misali da nasarorin Salah a matsayin gaskiya da jajircewa.

Dan lokacin da Salah ya yi a Chelsea, zai iya kasancewa wani labarin yadda jajircewa ke kai mutum ga nasara ta hanyar dagewa har mutum ya goge.

Hanaa da Muhammad da miliyoyin yara, wannan zai iya zama darasi a gare su.

Muna da lokaci sosai da za mu ci gaba da kallo tare da ci gaba da yi wa wannan matashi addu'a a yayin da ya kama hanyar zama fitaccen dan kwallo a duniya.