Andres Iniesta zai bar Barcelona a karshen kakar bana

Andres Iniesta Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Andres Iniesta ya lashe wa Barcelona Copa del Rey sau hudu a jere

Kaftin din Barcelona, Andres Iniesta, ya ce zai bar kungiyar da ke kasar Spain a karshen wannan kakar.

Dan wasan na tsakiya, mai shekara 33, ya buga wasanni 669, inda ya ci kofi 31 a Barcelona.

Iniesta kuma ya ci wa Spain kofin duniya da kofin Turai guda biyu.

Ya kasance muhimmin dan wasa a Barcelona, inda a nan ne ya fara taka leda tun kuriciyarsa.

A lokacin da yake bayar da sanarwar cewa zai bar kungiyar, Iniesta ya ce "wannan wata rana ce mai wahala a gare ni"

Iniesta, ya buga wa Spain wasanni 125, kuma yana cikin 'yan wasan kasar da za su buga gasar cin kofin duniya a Rasha a bana.

Ya ci gasar cin kofin duniya a shekarar 2010 da gasar cin kofin kasashen Turai a 2008 da kuma 2012 - baya ga gasar zakarun Turai hudu da kuma gasar La Liga takwas da ya lashe - tare da wasu kofuna da dama da ya ci wa Barcelona.

Nasarorin Iniesta

A Barcelona da Spain

669

Wasan da ya buga wa Barcelona

125

Wasan da ya buga wa Spain

  • 31 Yawan kofin da ya lashe a Barca

  • 3 Kofin da ya ci wa Spain

  • 456 Wasannin da ya yi nasara a Barcelona

  • 85 Wasannin da ya yi rashin nasara a Barcelona. Ya yi canjaras 128

Getty

Labarai masu alaka