Zakarun Turai: Fatan Chelsea ya karu bayan cin Swansea 1-0

Cesc Fabregas lokacin da ya ci Swansea Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Cesc Fabregas ne dan Spaniya na uku da ya ci bal hamsin a gasar Premier bayan Fernando Torres da Diego Costa

Chelsea ta kara kaimi a kokarinta na samun gurbin zuwa gasar zakarun Turai bayan da ta je gidan Swansea ta doke ta 1-0, ya rage maki biyu ke tsakaninta da ta hudu Tottenham.

Kociyan kungiyar wadda ya rage mata wasa uku, Antonio Conte ne ya bayyana haka, bayan wasan da Cesc Fabregas ya ci bal dinsa ta 50 a gasar ta Premier.

A ranar Litinin ne Tottenham ta hudu a tebur da maki 68, a wasa 34 za ta yi kwantan wasanta daya da Watford.

Conte ya ce, ikon ba a hannunsu yake ba, amma hanya daya da za su dan matsa wa Tottenham ita ce su samu maki uku a kowa ne wasa.

Amma kuma ya kara da cewa ba abu ne mai sauki ba ka ci kowa ne wasa a gasar ta Premier.

Yanzu Swansea ta na gaban Southampton da maki daya ne kawai a rukunin masu faduwa daga Premier bayan da Swansean ta ci Bournemouth 2-1, a karawarsu su ma ta Asabar.

Wannan sakamako ya sama wa West Brom sauki domin da za ta fadi daga gasar Premier idan da Swansea ta yi canjaras.

Yanzu Swansea a wasa na gaba za ta je wa Bournemouth ranar Asabar mai zuwa yayin da Chelsea a gidanta za ta kara da Liverpool, ranar Lahadi ta gaba, a wasan da ke da matukar muhimmanci a kokarinta na samun gurbin zuwa gasar zakarun Turan.

Sakamakon Wasannin na Premier na Asabar:

Liverpool 0-0 Stoke

Burnley 0-0 Brighton

Crystal Palace 5-0 Leicester

Huddersfield 0-2 Everton

Newcastle 0-1 West Brom

Southampton 0-2 Bournemouth

Swansea 0-1 Chelsea

Wasannin ranar Lahadi:

West Ham da Manchester City

Manchester United da Arsenal