DR Congo: Kotun Soji ta yanke wa madugun 'yan tawaye daurin shekara 20

Kungiyar Trail International ta ce Maro Ntumwa ya aikata wadanan laifuka ne shekara 10 da suka gabata Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kungiyar Trail International ta ce Maro Ntumwa ya aikata wadanan laifuka ne shekara 10 da ta gabata

Wata kotun Soji a Jamhuriyar Dumokuradiyar Congo ta aike da wani magudun 'yan tawayen kasar zuwa shekara 20 a gidan kaso bayan samunsa da aikata laifukan yaki shekara 10 da ta gabata.

An sami Maro Ntumwa, wanda aka fi sani da ''The Moroccan'' da laifukan da suka hada da fyade, da bautarwa ta hanyar lalata, da kai hare-hare a kan fararen hula a gabashin kasar.

Kungiyar Trial International, wadda ke taimaka wa wadanda aka gallazawa da gabatar da shaidu a kan cin zarafi, ta ce Ntumwa ya ci zarafin daruruwan mutanen kauyuka tsakanin 2005-2007.

Kuma a cewar Kungiyar, ya jagoranci kungiyar miyagu, da ke garkuwa tare da azabtar da maza da mata, da kuma dauresu a jikin bishiya ko jefa su cikin ramuka.

Trail International, ta Kuma ce Kotu ta umarci a biya diyya tsakanin dala dubu 2 zuwa 5 ga kowanne mutum da ya fuskanci irin wannan cin zarafin.

Arewa da Kudancin lardunan Kivu sun fuskanci karuwar rikici tsakanin kungiyoyin mayaka, da a lokuta da dama ke kwatar kudade daga fararen hula ko fada da juna a kan iko da albarkatun kasar ta Congo.

Labarai masu alaka