Barcelona ta dauki kofin La Liga na bana

Andres Iniesta da sauran 'yan wasan Barcelona bayan doke Deportivo La Coruna 4-2 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Andres Iniesta ya dauki kofin La Liga a karo na tara, wanda shi ne ya kasance kofi na 32 kuma na karshe da ya dauka da Barca, saboda zai bar kungiyar a karshen kakar nan

Barcelona ta ci kofin La Liga na 25 a kakar farko ta kociya Ernesto Valverde bayan da Lionel Messi ya taimaka ta doke Deportivo La Coruna 4-2.

Messi ya ci kwallo uku rigios a wasan da Barca ta yi fintinkau da ratar da ba za a kamo ta ba a teburin gasar da maki 86 a wasanta 34.

Barcelona ce ta fara shiga gaba a wasan da ci 2-0 sakamakon kwallayen da Philippe Coutinho da Messi suka zura.

Sai dai 'yan Depor sun tashi tsaye inda suka farke balabalan ta hannun Lucas Perez and Emre Colak.

A cikin minti goman karshe ne na wasan Messi ya zura biyu, wasan ya kasance 4-2.

Wannan shi ne kofin La Liga na 25 da Barcelona ta dauka, bambancin takwas tsakaninta da abokiyar hamayyarta Real Madrid.

Wasa hudu ya rage a kammala gasar da har yanzu ba a doke Barcelonar ba.

Matsayin wasan ga Andres Iniesta

Wasan shi ne na farko tun bayan da Andres Iniesta ya sanar da cewa zai bar kungiyar ta Barcelona a karshen kakar nan.

Dan wasan na tsakiya mai shekara 33 ya kasance a benci lokacin da aka fara, daga baya kociyansu Valverde ya sako shi a minti na 87, inda magoya bayan kungiyoyin biyu suka yi ta masa tafi.

Ranar Lahadi mai zuwa za ta kasance dama ta karshe da Iniesta zai yi wasan hamayya na El Clasico lokacin da Real Madrid za ta ziyarci Nou Camp.

Bayan wasan za kuma su kara a gida da Villarreal sannan su je Levante, kafin karshen wasansa a Barca wanda Real Sociedad za su ziyarce su a Nou Camp ranar 20 ga watan Mayu.

Sauran Wasannin La Liga da aka yi ranar Lahadi:

Atletico Madrid ta ci gaba da zama ta biyu a tebur da tazarar maki takwas tsakanin da da Barca, bayan da ta bi Alaves gida ta doke ta da ci 1-0.

A ranar Alhamis Atletico za ta karbi bakuncin Arsenal wasansu na biyu na Europa bayan da suka yi 1-1 a karawar farko a Emirates.

Getafe 1-1 Girona

Valencia 0-0 Eibar

Labarai masu alaka