Sau nawa Real Madrid na fitar da Bayern Munich a zakarun Turai?

'Yan wasan bayern Munich Hakkin mallakar hoto Bayern Munich
Image caption Tuni 'yan wasan Bayern Munich suka isa Madrid domin wannan wasan

Bayern Munich da Real Madrid za su fafata a wasa na biyu na dab da na karshe a gasar cin kofin zakarun Turai.

Real ta yi nasara a wasan farko da ci 2-1 wanda aka yi a filin wasa na Allianz Arena da ke Munich, Jamus.

Wannan ne karo na 27 da suka kara da juna a gasar Turai - kuma ita ce haduwa mafi yawa da aka taba yi tsakanin wasu kungiyoyi biyu.

Real Madrid ta samu nasara sau 12 yayin da Bayern ta ci karawa 11 a tarihin haduwarsu.

Wannan shi ne karo na uku tun shekarar 2011-12 da Bayern da Real suka hadu da juna a wasan dab da na karshe.

Bayern ta samu nasara a 2011-12 yayin da Madrid ta kai ga ci a 2013-14.

Bayern ta sha kashi a wasanninta biyar na baya-bayan nan da ta fafata da Madrid a gasar zakarun Turai.

Kocin bayern Jupp Heynckes ya samu nasara a wasa 14 cikin 16 da ya buga a filin wasa na Allianz Arena a gasar zakarun Turai (canjaras daya, rashin nasara daya), inda Bayern ta zura kwallo 48 sannan aka ci ta 10.

Bajintar Cristiano Ronaldo

Ya fi kowa cin kwallo a gasar Turai

42

Kwallon da ya zura a kakar bana a dukkan wasannin da ya buga

120

Kwallon da ya zura a tarihin gasar zakarun turai

  • 28 Kwallon da ya zura a wasa 13 a jere na baya-bayan nan

  • 15 Kwallon da ya zura a gasar zakarun turai ta bana

  • 9 Kwallon da ya zura a ragar Bayern Munich

  • 13 Kwallon da ya zura a wasannin dab da na karshe a gasar

Cristiano Ronaldo ya zura akalla kwallo daya a duk wasa 11 na baya-bayan nan da ya buga a gasar (kwallo 17 jumulla).

Wannan ita ce bajinta mafi kyau da wani dan wasa ya taba yi a tarihi.

Dan wasan mai shekara 33 ya ci kwallo tara a ragar Bayern Munich a gasar zakarun Turai.

Shi ne dai dan wasa daya tilo da ya ci kwallo fiye da haka a ragar wata kungiya, inda ya zura kwallo 10 a ragar Juventus.

Wannan wasa zai kuma hada 'yan wasan da suka fi kowa zura kwallo a wasan dab da na karshe na gasar- Cristiano Ronaldo ya zura 13 a wannan mataki, yayin da Robert Lewandowski ya ci shida.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ronaldo da Lewandowski sun fi kowa zura kwallo a wasannin dab da na karshe a tarihin gasar zakarun Turai