Kalli atisayen Real Madrid na karshe kafin wasan Bayern Munich

'Yan wasan Real Madrid sun yi atisaye na karshe kafin wasansu da Bayern Munich a wasan dab da na karshe na gasar zakarun Turai.

Real ta yi nasara a wasan farko da ci 2-1 wanda aka yi a filin wasa na Allianz Arena da ke Munich, Jamus.

Wannan ne karo na 27 da suka kara da juna a gasar Turai - kuma ita ce haduwa mafi yawa da aka taba yi tsakanin wasu kungiyoyi biyu.

Ga wasu daga cikin hotunan 'yan wasan Madrid a lokacin atisayen nasu na karshe kafin wasan:

Hakkin mallakar hoto Real Madrid
Image caption Cristiano Ronaldo ne ya ja ragamar gaban Real Madrid - ya shafe wasa tara yana cin kwallo a jere a filin wasan na Bernabeu
Hakkin mallakar hoto Real Madrid
Image caption Kusan duka 'yan wasan Madrid lafiyarsu kalau kuma sun yi atisaye
Hakkin mallakar hoto Real Madrid
Image caption Dani Cavajal ne kawai ba zai buga ba saboda raunin da ya samu a wasan farko a Jamus
Hakkin mallakar hoto Real Madrid
Image caption Baya ga Ronaldo, ana sa ran Bayern za su mayar da hankali sosai kan matashin dan kwallon Real Marco Asensio

A nasu bangaren Bayern Munich, tuni suka isa birnin Madrid, kuma sun ce suna da kwarin gwiwar doke Madrid domin kai wa wasan kasrhe.

Ga hotunan wasu daga cikin 'yan wasan na Bayern bayan isar su birnin Madrid:

Hakkin mallakar hoto Bayern Munich
Image caption A bara ma Real Madrid ce ta fitar da Bayern - a don haka za su so yin ramuwar gayya
Hakkin mallakar hoto Bayern Munich
Image caption 'Yan wasan bayern Munich sun ce suna sa ran nuna Madrid cewa sa'a kawai ta samu a wasan farko
Hakkin mallakar hoto Bayern Munich
Image caption James Rodriguez, wanda dan wasan Madrid ne da ya je Bayern a matsayin aro, ya ce ba zai yi murna ba idan ya ci Madrid a wasan