Arsenal ta yi ban kwana da kofin Europa na bana

Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Arsenal ba za ta buga Champions League a badi ba

Atletico Madrid ta kai wasan karshe a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Europa, bayan da ta ci Arsenal 1-0 a Spaniya a ranar Alhamis.

Atletico ta buga kunnen doki 1-1 da Arsenal a Emirates, inda ta ci 1-0, jumulla ta ci kwallo 2-1 karawar da suka yi gida da waje kenan.

A karshen kakar nan Arsene Wenger zai bar Arsenal, bayan shekara 22 da ya yi yana jan ragamar Gunners, kuma bai taba cin kofin Zakarun Turai ba.

Atletico ta lashe Europa karo biyu a tarhi, za kuma ta buga Champions League a badi, tana ta biyu a kan teburin La Liga da maki 75, saura wasa uku a kammala gasar Spaniya ta bana.

Ita kuwa Arsenal karo biyu kenan a jere ba za ta gasar Zakarun Turai ta badi ba, domin tana ta shida a teburin Premier shekarar nan.

Labarai masu alaka