Yaya Toure zai bar Manchester City a karshen kaka

Yaya Toure and Pep Guardiola Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yaya Toureya buga wa Manchester City wasanni 16 a wannan kakar

Dan wasan tsakiyar Manchester City, Yaya Toure, zai bar zakaran gasar Firimiya ta bana a karshen wannan kakar.

Dan wasan mai shekara 34 zai buga wasansa na karshe a Man City ranar Laraba lokacin da kungiyar za ta kara da Brighton, in ji koci Pep Guardiola.

Dan wasan kasar Ivory Coast Toure, wanda ya koma City daga Barcelona kan kudi fam miliyan 24 a shekarar 2010, ya rattaba hannu a kan yarjejeniyar shekara daya a watan Yunin shekarar 2017.

"Yaya ya zo nan a farkon wannan tafiyar," in ji Guardiola. "Muna inda muke ne a yanzu saboda abin da ya yi."

"Ba za mu iya manta abin da ya kama daga lokacin Roberto Mancini ba, musamman lokacin Manuel Pellegrini, Yaya ya kasance muhimmin dan wasan lokacin.

"A karawarmu da Brighton za mu ba shi abin da ya dace da shi, bankwana mai matukar kyau da ko wane dan wasa zai so ya samu.

"Za mu mayar da hankali kan samun nasara saboda Yaya, za mu yi kokarin yi masa wannan."

Labarai masu alaka