Steven Gerrard ya zama sabon kocin Rangers

Steven Gerrard da shugaban Rangers Dave King Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaban Rangers ya yi imani da Steven Gerrard

Kungiyar Rangers ta Scotland ta nada Steven Gerrard a matsayin sabon kocinta.

Tsohon kaftin din na Liverpool ya amince da yarjejeniyar shekara hudu da kungiyar.

Gerrard zai fara aikin horar da Rangers ne a kaka mai kamawa.

Tsohon dan wasan na Ingila mai shekaru 37 ya yi alkawarin kayatar da magoya bayan Rangers.

Gerrard ya zabi tsohon kafin din Scotland Gary McAllister a matsayin wanda zai taimaka ma sa a aikin horar da kungiyar.

Steven Gerrard ya lashe kofuna tara a wasanni 710 da ya bugawa Liverpool a shekara 19, sannan ya buga wa Ingila wasa 114.

A 2016 ne ya yi ritaya daga tamaula bayan ya koma LA Galaxy a Amurka.

Gerrard yanzu ya gaji Graeme Murty ne da Rangers ta ba rikon kwarya.

Labarai masu alaka