Shin ina Andres Iniesta zai koma ne?

Andres Iniesta Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Iniesta ya lashe kofi 32 a Barcelona

Kungiyoyin kwallon kafa da dama musamman a Turai sun fara zawarcin Kaftin din Barcelona Andres Iniesta.

Har yanzu fitaccen dan wasan na Spain bai bayyana makomarsa ba a kwallon kafa bayan ya sanar da zai bar Barcelona idan an kammala kaka.

Wasu rahotanni na alakanta dan wasan da Manchester City saboda tsohon kocinsa Pep Guardiola, da kuma Paris St-Germain da ake ganin za ta yi gaggawa karbe dan wasan.

Arsenal ma na cikin kungiyoyin da ake ganin za ta bukaci dan wasan mai shekaru 33, musamman idan tsohon kocin Barcelona Luis Enrique ya karbi aikin horar da kulub din.

An fi alakanta dan wasan da China inda rahotanni suka ce an shafe tsawon shekara yana tattauna yiyuwar komawa da taka-leda a Lig din kasar.

Amma zuwa yanzu rahotanni na nuna babu tabbas kan yiyuwar komawar Iniesta China, saboda yadda manyan kungiyoyin Turai suka nuna suna bukatar dan wasan.

Wasu rahotanni sun ce tuni manyan kungiyoyi Turai guda hudu suka mika bukatarsu ga Iniesta da kuma kudin da za su biya shi.

Tun da farko an ruwaito cewa Iniesta zai koma China ne da taka leda saboda cimma wasu bukatunsa na kasuwanci.

Kuma a lokacin da yake bayyana cewa zai bar Barcelona, Iniesta ya ce nahiyar Turai ba ta cikin lissafinsa saboda ba zai iya hamayya da Barcelona ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Iniesta ya zubar da kwalla a lokacin da yake sanar da zai bar Barcelona

Dan wasan ya ce sai a karshen kaka zai sanar da makomarsa.

Iniesta ya shafe rayuwarsa ne a Barcelona, kuma yana cikin 'yan wasan da suka fi samun nasarori a kulub din.

Ya lashe kofin La liga 32 a kakar wasanni 16, sannan ya ci kwallo 57 a wasanni 669.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A wasan Barcelona da Sevilla Andres Iniesta ya nuna har yanzu kwallo na yinsa,

Labarai masu alaka