Marcelo's son pulls off AWESOME header trick with Real Madrid squad
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kalli yadda dan Marcelo ya nuna bajinta a cikin 'yan wasan Real Madrid

Idan mahaifinka na taka-leda a Real Madrid, kuma kana bukatar mutanen da za su taimaka maka yin atisaye domin nuna kwarewarka a fagen kwallo, to hakika ka caba.

Kalli wannan bidiyon na dan gidan Marcelo Vieira, inda ya rinka gara kwallo da ka da shi da 'yan wasan Real Madrid a dakinsu na canza kayan kwallo!

Dan kwallon na Real Madrid ya wallafa bidiyon a shafinsa na Instagram yana mai cewa ya yi matukar alfahari da bajintar dan nasa.

Kawo yanzu miliyoyin mutane ne suka kalli bidiyon a shafukan sada zumunta.

Abin da zai dauki mutum wani dan lokaci yana gwaji kafin ya iya yin hakan:

Labarai masu alaka