Eden Hazard zai iya barin Chelsea - Steve Clarke

Hazard Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Eden Hazard ya taimakawa Chelsea lashe kofin FA bayan ya ci Man Utd a faneriti

Chelsea na iya sayar da Eden Hazard don ta samu kudaden sayen sabbin 'yan wasa, a cewar Steve Clarke tsohon mataimakin kocin Kulub din.

Hazard mai shekara 27 shi ne ya taimaka wa Chelsea daukar kofin FA a Wembley a ranar Asabar bayan da ya zura kwallo a bugun fanariti a ragar Manchester United inda aka tashi 1-0.

Chelsea ba za ta buga gasar Zakarun Turai ba kaka mai zuwa bayan kammala Premier tana matsayi na shida a tebur.

Tsohon mataimakin kocin kungiyar Steve Clarke ya ce dole Chelsea na bukatar zubin sabbin 'yan wasa.

Mista Clarke ya ce abu mai yiyuwa ne Hazard ya bar Chelsea idan an bude kasuwar musayar 'yan wasa.

Shekaru biyu suka rage yarjejeniyar Hazard ta kawo karshe da Chelsea.

A shekarar 2012 ne Chelsea ta dauko Hazard daga Lille. Dan wasan na Blegiumya karbi kyautar gwarzon dan wasan Ingila a shekarar 2015 da ya lashe kofin Premier.

Tuni golan Chelsea Thibaut Courtois ya bukaci shugabannin Kulub din su yi zubin sabbin 'yan wasa.

Akwai yiyuwar golan dan kasar Belgium zai bar Chelsea idan kwangilar shi ta kawo karshe da kungiyar.

Labarai masu alaka