Iniesta ya yi kukan barin Barcelona

Andres Iniesta is thrown into the air by his Barcelona team-mates Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Barcelona ta yaba wa Andres Iniesta da wani dogon shiri bayan wasan

Andres Iniesta ya kammala taka leda a Barcelona, inda kungiyar ta samu nasara a kan Real Sociedad a wasansa na karshe.

Dan wasan tsakiyar na Spaniya, mai shekara 34, zai bar zakarun La Liga ne a karshen wannan kakar, bayan ya lashe manyan wasanni 22 da manyan 'yan wasan kulob din cikin shekara 16.

'Yan kallo sun rika daga wani sako da ke cewa: "Sai Iniesta har abada" kafin a fara wasan.

Iniesta ya taka rawa daidai gwargwado yayin wasan, inda Barcelona ta kammala kakar da nasara ta hanyar kwallon da Philippe Coutinho ya zura a raga.

Tsohon dan wasan tsakiyar Liverpool din ya zura kwallo a raga ne a minti na 57.

An maye gurbin Iniesta, wanda ya jagoranci kungiyar, a minti 82 da fara wasan, inda ya rungumi dukkan 'yan wasan kungiyarsa kuma ya gai da magoya bayansu a Nou Camp, a cikin hawaye.

Bayan an kammala wasan, filin wasan ya yi duhu kafin fitulu su dawo lokacin da 'yan wasan Barcelona suka fito suna sanye da rigar Iniesta domin su yi masa tsayuwar ban girma.

Daga nan sai Iniesta da kansa ya fito waje kuma ya daga kofin La Liga da na Copa del Rey.

Karo na hudu ke nan da ya lashe dukkanninsu a cikin kaka daya, kafin ya gabatar da wani jawabi ga jama'a.

"Wannan wata rana ce mai wuya a gare ni, amma na shafe shekara 22 masu ban mamaki a nan," in ji shi.

"Ina cike da alfahari da farin ciki domin kare da kuma wakiltar wannan kulob din, wanda a gare ni shi ne ya fi ko wanne a duniya."

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Magoya bayan Barcelona sun rubuta sako mai cewa 'Iniesta har abada' kafin a fara wasan
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An sauya Iniesta saura mintuna takwas a tashi wasan
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wannan ne wasa na 674 da ya yi wa Barcelona

Labarai masu alaka