An fitar da 'yan wasan da za su buga wa Spaniya kofin duniya

Alvaro Morata last played for Spain in November 2017 when he scored against Costa Rica in a friendly

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Alvaro Morata ya buga wa Spaniya wasa na karshe ne a watan Nuwambar 2017 a lokacin da ya ci Costa Rica a wasan sada zumunta

Babu dan wasan Chelsea Alvaro Morata a jerin 'yan wasa 23 da Spaniya ta fitar da za su wakilce ta a gasar cin kofin duniya ta Rasha 2018.

Dan kwallon mai shekara 25 ya zura kwallo 11 a kakar farko da ya yi a Stamford Bridge kuma sai a mintin karshe aka sako shi a wasan karshe na cin kofin FA da Chelsea ta buga ranar Asabar.

Koci Julen Lopetegui ya bayyana sunayen 'yan wasa hudu da ke taka-leda a gasar Firimiya da suka hada da David De Gea, David Silva, Cesar Azpilicueta da kuma Nacho Monreal.

Spaniya za ta fara wasanta na farko da Portugal a ranar 15 ga watan Yuni a birnin Sochi.

Ga jerin 'yan wasan da Spaniya za ta fita da su fagen daga:

Masu tsaron raga:

David de Gea (Manchester United), Pepe Reina (Napoli), Kepa Arrizabalaga (Athletic Bilbao).

Masu tsaron baya:

Jordi Alba (Barcelona), Nacho Monreal (Arsenal), Alvaro Odriozola (Real Sociedad), Nacho Fernandez (Real Madrid), Dani Carvajal (Real Madrid), Gerard Pique (Barcelona), Sergio Ramos (Real Madrid), Cesar Azpilicueta (Chelsea).

'Yan tsakiya:

Sergio Busquets (Barcelona), Isco (Real Madrid), Thiago Alcantara (Bayern Munich), David Silva (Manchester City), Andres Iniesta (Barcelona), Saul Niguez (Atletico Madrid), Koke (Atletico Madrid).

Masu cin kwallo:

Marco Asensio (Real Madrid), Iago Aspas (Celta Vigo), Diego Costa (Atletico Madrid), Rodrigo Moreno (Valencia), Lucas Vazquez (Real Madrid).