Unai Emery ne zai gaji Arsene Wenger a Arsenal

  • Daga David Ornstein
  • BBC Sport
Unai Emery

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Unai Emery na daf da zama sabon kocin Arsenal bayan shafe shekara biyu a Paris St-Germain

Arsenal na daf da nada Unai Emery a matsayin sabon kocin kulob din domin ya gaji Arsene Wenger.

A baya an yi tsammanin cewa mataimakin kocin Manchester City kuma tsohon kyaftin din Gunners Mikel Arteta ne zai samu mukamin.

Amma Emery ya zamo mutumin da aka yi ittifaki a kansa bayan an tattauna da dukkan mutanen da suka nemi aikin.

Ana sa ran nan gaba a wannan makon ne za a bayyana nadin nasa.

Kocin mai shekara 46 dan kasar Spaniya ba shi da kulob bayan da ya bar Paris St-Germain a karshen kaka, inda ya lashe gasar Ligue 1 da kuma kofunan cikin gida hudu a shekara biyu da ya shafe a can.

A baya ya jagoranci Sevilla inda ta lashe kofin Zakarun Turai na Europa sau uku a jere tsakanin 2014 zuwa 2016.

Tuni PSG ta sanar da nadin tsohon kocin Borussia Dortmund Thomas Tuchel a matsayin wanda zai maye gurbinsa.