Paul Pogba a Umarah: Dakin Allah wuri ne na musamman

Dan wasan kulob din Manchester United Paul Pogba ya tafi kasar Saudiyya don fara aikin Umarah a watan Ramadan, 'yan kwanaki kadan kafin fara Gasar Cin Kofin Duniya a kasar Rasha.

Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Instagram a ranar Talata, Pogba ya ce "yana fatan duk wanda bai taba zuwa Umarah ba, wata rana zai yi hakan."

"Ba karamin lamari ba ne mai dadi mutum ya samu kansa a nan wurin... Dakin Allah wuri ne na musamman," in ji Pogba.

Dan kwallon na kasar Faransa na shirin tafiya kasar Rasha domin bugawa kasarsa kwallo a gasar cin kofin duniya da za a fara a watan gobe.

Ba wannan ne karon farko da dan wasan kasar Faransar yake zuwa Umarah ba, don ko a bara ya kai ziyara kasar Saudiyya lokacin watan azumin Ramadan.

Rahotannin kafafen yada labarai sun ce Pogba, wanda dan kasar Faransa ne, yana yin ibadarsa ta addinin Musulunci.

Pogba wanda da ma Musulmi, ya koma United a shekarar 2016 daga Juventus a matsayin dan wasan da ya fi kowanne tsada a duniya.

Hotunan dan wasan lokacin da yake aikin Umarah bara:

Bayanan hoto,

Ɗan wasan ya ce yana yi wa Musulmi barka da azumi.

Bayanan hoto,

Pogba ne dan wasan da ya fi tsada a duniya a shekarar 2017