Atletico Madrid ta doke Najeriya

Atletico Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Atletico Madrid ita ce ta lashe kofin zakarun Turai na Europa League na bana

Kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta Spaniya ta doke Najeriya da ci 3-2 a wani wasan sada zumunta da suka buga a kasar ranar Talata.

'Yan wasan Super Eagles ne suka fara zura kwallo a ragar Atletico Madrid a minti na 32 da fara wasan, kafin Angel Correa ya farke kwallon a minti na 33.

Wasan ya koma 2-1 ne a minti na 64, bayan da Fernando Torres ya zura kwallo a ragar Najeriya. Sai dai an farke kwallon a minti 80, inda wasan ya koma 2-2.

Amma kuma Atletico Madrid ta kara zuwa Najeriya kwallo a raga ana saura minti 10 a tashi wasan.

A ranar Litinin ne da daddare 'yan wasan na Atletico, wadanda su ne zakarun Turai na Europa League, suka isa birnin Uyo na jihar Akwa Ibom don fafatawa a wasan.

An yi wasan sada zumuntar ne a wani bangare na shirye-shiryen da kasar ke yi domin tunkurar gasar cin kofin duniya, wadda za a fara a watan gobe a kasar Rasha.

Labarai masu alaka