Unai Emery ya ce magoya bayan Arsenal za su ji dadi

Unai Emery
Bayanan hoto,

Unai Emery ya komo Arsenal ne bayan shafe shekara biyu a Paris St-Germain

Sabon kocin Arsenal, Unai Emery, ya ce yana sa ran kayatar da dukkan magoya bayan Arsenal.

Kocin, wanda ya fadi haka bayan an tabbatar da cewar shi ne zai maye gurbin Arsene Wenger, ya ce yana matukar farin cikin jan ragamar kulob din "a wannan sabon lokaci na tarihinsa".

"Ina matukar farin cikin komawa daya daga cikin manyan kulob na wasan kwallon kafa.

An san Arsenal da salon wasanta a fadin duniya da kuma yadda take bai wa kananan 'yan wasa fifiko da filin wasanta mai burgewa da kuma yadda ake gudanar da kulob din."

Kocin dai ya ce yana da karfin gwiwa akan abin da shi da kulob din da magoya baya za su iya cimma wa tare.

Bayanan hoto,

Tuni Emery ya sauya bayanan da ke shafinsa na Twitter jim kadan bayan nada shi

Kocin mai shekara 46 dan kasar Spaniya ba shi da kulob tun bayan da ya bar Paris St-Germain a karshen kaka, inda ya lashe gasar Ligue 1 da kuma kofunan cikin gida hudu a shekara biyu da ya shafe a can.

A baya ya jagoranci Sevilla inda ta lashe kofin Zakarun Turai na Europa sau uku a jere tsakanin 2014 zuwa 2016.

Tuni PSG ta sanar da nadin tsohon kocin Borussia Dortmund Thomas Tuchel a matsayin wanda zai maye gurbinsa.