Kalli manyan 'yan wasan Turai da ba su ci kwallo ba a bana

Ko akwai 'yan wasa da ba su zura kwallo a raga ba har aka kammala wasannin Lig lig na Turai a bana?

Za ku yi mamaki idan kuka ga wasu daga cikinsu musamman ganin irin rawar da suka saba takawa a baya.

Kuna iya duba wannan kalandar da ke kasa tare da ci gaba da latsa " na gaba" don ganin wasu daga cikin manyan 'yan wasan Turai da ba su zura kwallo a raga ba har aka kammala kakar bana.

2017/2018

 • Yaya Toure - Manchester City
  Yaya Toure

  Yaya Toure bai ci kwallo ba a dukkanin wasannin da ya buga a kakarsa ta karshe a Manchester City. Dan wasan na tsakiya ya ci kwallo 62, ya taimaka an ci 32 a wasa 230 da ya buga a rayuwarsa a Manchester City.

  Karin bayani a nan

 • Michael Carrick - Manchester United
  Hoton Michael Carrick

  An kammala kakar 2017/2018 ba tare da kaftin din na Manchester United ya zura kwallo a raga ba. Dan wasan tsakiyar mai shekara 36 wanda ya sanar da yin ritaya a karshen kaka, ya buga wasa 463 inda ya lashe kofi 12 a shekara 12 a Manchester United.

  Karin bayani a nan

 • Yohan Cabaye – Crystal Palace
  Hoton Yohan Cabaye

  Dan wasan na tsakiya ya buga wasa 30 a kakar bana amma ba tare da ya zura kwallo a raga ba, amma ya taimaka an ci kwallo daya. Cabaye ya ci kwallaye 26 a wasa 174 da ya buga a gasar Premier.

  Karin bayani a nan

 • Gabi - Atletico Madrid
  Gabi - Atletico Madrid

  Dan wasan na Spain ya buga wa Atletico Madrid wasa 51 amma ba tare da ya zura kwallo a raga ba. Sai a wasan karshe a gasar Europa dan wasan na tsakiya ya zura kwallo a raga. Gabi ya taka-leda sau 400 a La liga a Atletico Madrid da kuma Zaragoza.

  Karin bayani a nan

 • Mateo Kovacic - Real Madrid
  Mateo Kovacic

  Dan wasan na tsakiya ya buga wa Real Madrid wasa 32 a kakar 2017/2018 amma ba tare da ya ci kwallo ba a raga. Ko da yake ba kasafai Zidane ke fara wasa da dan wasan na Croatia ba.

  Karin bayani a nan

 • Sulley Muntari - Deportivo La Coruna
  Sulley Muntari

  Sulley Muntari na cikin 'yan wasa a Turai da aka kammala kaka ba tare da sun ci kwallo ba. Ko da yake Kocin Deportivo Clarence Seedorf ya dauko dan wasan na Ghana kuma tsohon dan wasan Inter Milan da AC Milan ne a watan Fabrairun 2018 domin ya taimaka ma sa.

  Karin bayani a nan

 • Lassana Diarra - PSG
  Lassana Diarra

  Dan wasan na tsakiya ya buga wa PSG wasa 19 a kakar 2017/18 ba tare da ya ci kwallo ba. Diarra ya taka leda a manyan kungiyoyin Turai da suka hada da Real Madrid da Chelsea da Arsenal.

  Karin bayani a nan

 • Okechukwu Azuibuike – Yeni Malatyaspor
  Okechukwu Azuibuike

  Azuibuike dan Najeriya ne da ke taka-leda a kulub din Malatyaspor na Turkiyya. Dan wasan na tsakiya ya buga wasa 26 a kakar 2017/18 ba tare ya zura kwallo a raga ba.

  Karin bayani a nan

 • James Milner - Liverpool
  James Milner

  An kammala kakar bana ba tare da Milner ya zura kwallo a raga ba a wasa 33 da ya buga wa Liverpool. A kakar da ta gabata dan wasan ya ci kwallo bakwai a wasa 36 a Premier.

Hakkin mallaka

Getty Images, Wikimedia commons

Labarai masu alaka