Manchester United na nazarin rabuwa da Martial

Anthony Martial Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A shekara ta 2013 Anthony Martial ya koma United daga Monaco

Manchester United za ta saurari wadanda ke bukatar sayen Anthony Martial, amma ba ta son sayar da Bafaranshen ga abokan hamayyarta a Ingila.

Martial, mai shekara 22, ya fuskanci kalubale a bana a United, inda tun watan Janairu bai sake zura kwallo a raga ba.

Dan wasan ba ya cikin 'yan wasan da za su buga wa Faransa gasar cin kofin duniya, inda yanzu babu tabbas game da makomarsa.

Jaridar Daily Mail ta fahimci cewa Manchester United za ta ba Martial damar ya tafi, kuma za ta fi son ya tafi wata kungiya a wajen Ingila.

Ana ganin Chelsea za ta bukaci dan wasan, kamar yadda Jose Mourinho ke son ya karbo Willian daga Chelsea.

Amma Manchester United za ta fi son Martial wanda ta dauko daga Monaco a 2013 kan fam miliyan 58, ya koma wata kungiya a Turai ba Ingila ba.