Mohamed Salah ba zai 'karya azumi' saboda wasan Real Madrid ba

Mohamed Salah
Bayanan hoto,

Mohamed Salah ne ya fi kowa cin kwallo a gasar Firimiya ta bana

Mohamed Salah zai iya yin azumin sa'a 18 kafin wasan karshe na gasar zakarun Turai inda kungiyarsa ta Liverpool za ta kara da Real Madrid.

Dan wasan dan kasar Masar, wanda Musulmi ne mai bin addini sau da kafa, ya yarda da azumin watan Ramadan wanda farilla ne yinsa daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana.

Wani rahoto a shafin intanet na El-Ahly ya yi ikirarin cewar Salah zai yi azumi ranar Asabar da za a yi wasan, kuma azumi zai kai sa'a 18.

Musulmin da ke Turai na yin azumi mafi tsayi idan aka kwatanta da sauran sassan duniya saboda bambancin lokaci.

Bayanan hoto,

Babu tabbacin ko takwaransa Sadio Mane zai yi azumi a ranar wasan

Sai dai kuma kawo yanzu babu tabbacin ko takwararsa Sadio Mane zai yi azumi a ranar wasan.

Mane Musulmi ne dan kasar Senegal, kuma yana bin addininsa sau da kafa.

Duka da cewa kocin Liverpool bai yi wani tsokaci ba game da yadda kungiyar za ta shirya Salah domin wasan, kocin tawagar kwallon kafar Masar, Hector Cuper, ya tattauna batun gabanin gasar cin kwallon duniya da za a yi a Rasha a watan gobe.

Cuper ya ce hukumar kwallon kafa ta Masar ta dauki wani kwararre da zai taimaki 'yan wasan kasar ga,e da yadda za su taka leda a lokacin azumik gabannin gasar cin kofin duniyar.