Andres Iniesta ya koma Japan da taka leda

Iniesta was presented with his shirt by Vissel Kobe owner Hiroshi Mikitani Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaban kulob din Vissel Kobe ya bai wa Iniesta riga mai lamba 8

Shahararren dan wasan Barcelona Andres Iniesta ya ce ya yi biris da tayin da wadansu kungiyoyi suka yi masa kafin ya amince ya koma kungiyar Vissel Kobe.

Dan wasan mai shekara 34 ya koma kungiyar da ke cikin rukuni na daya a kwallon kafar Japan ne bayan ya bar Barca, inda ya shafe shekara 22 yana taka leda.

"Kungiyoyi da dama sun yi zawarcina," in ji dan wasan kasar Spaniyar wanda rahotanni ke cewa zai karbi albashin dala miliyan 30 a kowace shekara.

"Na zabi zuwa Vissel Kobe ne saboda kungiya ce da nake sha'awa."

Ya kara da cewa: "Kuma an yarda da ni a matsayina na dan wasa - wannan ya kasance wani babban dalili."

Wanda ya mallaki kungiyar Kobe, Hiroshi Mikitani, ya ce Iniesta zai karfafa kungiyar kuma zai taimaka wa 'yan wasa masu tasowa.

Ya ce: "Na tuna salon tunanin Iniesta da shugabanci da kuma kwayoyin halitarsa na gado za su bayar da kwarin gwiwa wa Kobe da illahirin harkar kwallon kafa a Japan."

Mikitani ya kara da cewa: "Muna tsammanin Iniesta zai karfafa kungiyar tare da bayar da gudunmawa wajen ci gaban 'yan wasa masu tasowa ta hanyar shigar da dabarun Iniesta cikin makarantar koyar da kwallon kafa ta kungiyar.

"Mun yi imanin cewa hukuncin da ya yanke na koma wa Japan zai yi babban tasiri, ba wai akan Vissel Kobe ba kawai, har kan kwallon kafa a Japan da Asiya."

'Ina alfaharin ganin wannan rana'

Iniesta ya lashe kofuna 32 a Barcelona, inda ya buga wasa 674, yayin da ya fara wasa da bangaren karamar kungiyar a lokacin da yake dan shekara 12 a duniya.

Ya buga wasansa na karshe ne a Barcelona a ranar Lahadi a Gasar La Liga, inda suka doke Real Sociedad.

Dan wasan na Spaniya ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa shi zai je "sabon gidansa" ranar Laraba kuma shi zai hadu da tsohon dan wasan Arsenal da Jamus Lukas Podolski a Kobe.

Iniesta zai rika sa riga lamba 8 a sabuwar kungiyarsa yayin da sabuwar kungiyar tasa take mataki na 15 a gasar J-League bayan wasanni 15, kodayake ta kare ne ta tara a kakar da ta gabata.

Hakkin mallakar hoto Barcelona
Image caption Barcelona tweeted to wish their former player good luck
Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Iniesta lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Japan don kammala yarjejeniyar komawarsa can

Labarai masu alaka

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba