Za a yanke hukunci kan yin azumi ga 'yan kwallo

Goln Masar Essam El Hadary
Bayanan hoto,

Golan kasar Essam El Hadary ya ce za su yanke hukuncin ne gaba dayansu kan yadda za su tunkari batun azumin

Golan kasar Essam El Hadary ya ce za su yanke hukunci gaba dayansu kan ko za su yi azumi a watan Ramadan kamar yadda Musulunci ya tanada.

Azumin bana ya fado a lokacin da tawagar kasar ke shirin tunkarar gasar cin kofin duniya tare da yin wasannin share fage.

An fara azumin Ramadan, wanda a cikinsa Musumi ba sa ci ba sa sha daga hudowar rana zuwa faduwarta a ranar 16 ga watan Mayu, kuma zai kare ne a dai dai lokacin da ake fara gasar cin kofin duniya.

"Za mu gana da junanmu nan da 'yan kwanaki ma su zuwa, daga nan sai mu sanar da shugabanninmu matakin da muka dauka," a cewar El Hadary mai shekara 45.

Masar za ta kara da Kuwait a wasan share fage a karshen makon nan kafin sauran wasannin da za su yi da Colombia da Belgium.

Daga nan kuma sai su fara wasansu na farko a rukunin A ranar 15 ga watan Yuni da Uruguay kafin su kara da Rasha da Saudiyya.

Daraktan tawagar Ihab Leheta ya ce ba za a tilastawa kowanne dan wasa ba kan matakin da zai dauka.

Idan 'yan wasan suka yanke hukuncin cigaba da yin azumin, to tuni kociya Hector Cuper ya dauko masana da za su taimakawa 'yan wasan da tsarin cin abinci da kuma na barci.

Karin wasu labaran da za ku so ku karanta