Hotunan yadda Musulmin Amurka suka sha ruwa

BBC ta tattaro muku hotunan yadda wadansu Musulmi da ke kasar Amurka suka yi buda baki a ci gaba da azumin watan Ramadan.

Bayanan hoto,

Wani Musulmi lokacin da yake shan ruwa bayan faduwar rana a brinin New York na kasar Amurka ranar Laraba

Bayanan hoto,

Wadansu masu fafutika lokacin suke buda baki da wata kungiyar 'yan ci rani ta shirya a birnin New York na kasar Amurka ranar Laraba

Bayanan hoto,

Musulmi a Amurka suna kwashe kimanin sa'o'i 15 zuwa 16 na azumi wato tsakanin sahur da buda baki

Bayanan hoto,

Wata Musulma lokacin da take raba dabino a birnin New York ranar Laraba

Bayanan hoto,

Wadansu mata yayin da suke cin abinci bayan shan ruwa a birnin New York na kasar Amurka ranar Talata

Bayanan hoto,

Wadansu Musulmi mata lokacin da suke buda baki a cibiyar raya al'adu ta Eyup Sultan a birnin New York a makon jiya

Bayanan hoto,

Wadansu Musulmi lokacin buda baki a cibiyar addinin Karbala a jihar Michigan da ke Amurka ranar Juma'a

Bayanan hoto,

Jihar Michigan ita ce ta fi kowa ce jiha a kasar Amurka yawan Musulmi wadanda suka fito daga yankin Gabas Tsakiya

Bayanan hoto,

Wadansu mata Musulmi lokacin da suke sallar Magriba bayan shan ruwa a birnin New York na Amurka ranar Litinin