Zakarun Turai: Kalli hotunan atisayen Real Madrid da Liverpool

Liverpool da Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images

Liverpool da Real Madrid na shirin karawa a wasan karshe na gasar Zakarun Turai a birnin Kiev na Ukraine.

Wannan ne karo na farko da kungiyoyin biyu za su hadu a gasar, tun haduwarsu a 2014 a wasan rukuni inda Real Madrid ta yi nasara da ci 1-0.

Real Madrid na harin kare kofin wanda ta lashe sau biyu a jere, yayin da Liverpool za ta yi kokarin lashe kofin a karon farko tun kakar 2004-05 da ta lashe kofin a Istanbul.

Sau biyar Liverpool na lashe kofin gasar Zakarun Turai yayin da Real Madrid ta dauki kofin sau 12.

Ga wasu daga cikin hotunan atisayen 'yan wasan Liverpool da na Real Madrid a Kiev kafin wasan:

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Salah ya ci kwallaye 11 a gasar zakarun Turai a bana
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kwallaye 44 Salah ya ci a dukkanin wasannin da ya buga wa Liverpool a bana
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Liverpool ta fi yawan cin kwallaye a gasar zakarun Turai a bana inda ta ci 46
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Roberto Firmino da Sadio Mane da Mo Salah za su kasance babbar barazana ga Real Madrid
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dukkanin 'yan wasan Liverpool da za su kara da Real Madrid ba su taba buga wasan karshe ba a gasar Zakarun Turai
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Klopp zai yi kokarin huce hushin kashin da ya dade yana sha har sau biyar a wasannin karshe, ciki har da gasar Zakarun Turai a lokacin da yana Borussia Dortmund da kuma kashin da ya sha a hannun Sevilla a gasar Europa a 2016
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Real Madrid na harin lashe kofin gasar karo na uku a shekaru hudu
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ronaldo na harin lashe kofin gasar Zakarun Turai karo na biyar a rayuwarsa
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana tunanin Zidane zai ajiye Gareth Bale a benci ba zai fara da dan wasan na Wales ba
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Real Madrid ta kai wasan karshe bayan ta sha da kyar a hannun Juventus da Bayern Munich
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan wasan bayan Liverpool sai sun yi da gaske wajen rike Ronaldo kamar yadda 'yan wasan tsakiya za su yi fama da Isco da Casemiro da Toni Kroos da Luka Modric.
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Zidane na harin lashe kofin zakarun Turai karo na uku a jere a matsayin Koci

Labarai masu alaka