Za a sa rigunan Liverpool a Senegal saboda Mane

Sadio Mane

Sadio Mane ya aika da rigunan Liverpool 300 zuwa ga mutanen kauyensa a Senegal domin su saka a ranar da zai buga wasan karshe a gasar Zakarun Turai.

Dan wasan gaban mai shekara 26 wanda ya girma a Bambali cikin kasar Senegal, ya aika da sakon rigunan ne ga magoya bayansa a yayin da Liverpool ke shirin gwabzawa da Real Madrid a ranar Asabar a birnin Kiev na Ukraine.

Mane wanda musulmi ne, ya ce akwai mutane sama da 2,000 a kauyensa. "Na saye rigunan Liverpool 300 na aika zuwa kauyen domin mutane su saka a lokacin da suke kallon wasan," a cewarsa.

Ya ce mahaifiyarsa da danginsa dukkaninsu za su kalli wasan.

"Na san babu wanda zai yi wani aiki a ranar. Zan koma gida idan an kammala gasar cin kofin duniya, kuma ina fatan zan nuna wa kowa lambar yabon da na lashe."

A kauyensa, ne dai Mane ya kalli wasan da Liverpool ta rama kwallaye uku a ragar AC Milan kuma ta lashe kofin a 2005 - lokacin yana da shekara 13.

Mane ya ce wasan yana cikin wadanda ba zai taba mantawa ba duk da cewa a lokacin shi magoyi bayan Barcelona ne.

Dan wasan na Senegal wanda a karon farko zai buga wasan karshe a gasar Zakarun Turai ya ce yana fatar zai lashe kofin gasar.

Karin wasu labaran da za ku so ku karanta: