Mo Salah: Abin da ya sa Balaraben Masar ya gagari Turawa?

Mo Salah

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mo Salah ya ci kwallo 44 a wasa 50 da ya buga wa Liverpool a bana

A yayin da 'yan wasa ke murna kan nasarar da suka samu da ci 4-0 kan ENPPI, sai kocinsu Said Al Shesheni ya fahimci cewa akwai daya daga cikin tawagar Al-Mokawloon da ya nuna bai ji dadi sosai ba bayan wasan da aka yi a birnin Alkahira.

A zahirin gaskiya ma sai sharara kuka yake yi, damuwarsa shi ne babu sunan shi daga cikin wadanda suka ci kwallayen. Saboda yana buga lamba uku, zai yi wahala ya taka muhimmiyar rawa kamar yadda yake so.

Ya fito ne daga Nagrig, wani kauye da ke da nisan kilomita 130 da Al Kahira babban birnin Masar.

Dan wasan yakan shafe sa'o'i tara a rana yana kai-komo, wani lokaci yana hawan mota 10 kafin ya isa wurin atisaye.

Dan wasan ya ja hankalin kocinsa Al Shasheni inda ya ba shi dama ya mayar da shi dan wasan gaba.

Dan wasan da ake magana ba kowa ba ne illa Mohamed Salah, wanda tun a lokacin tauraronsa ke haskawa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Dan wasan na Liverpool ya samar da sabon filin wasa kusa da tsohuwar makarantarsa a Nagrig

Wannan labarin zai taimaka ya amsa tambayoyi da dama da ke zukatan masoya kwallon kafa a fadin duniya.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Shin ta yaya aka yi Mo Salah dan wasan da a baya ya fuskanci kalubale a manyan lig lig na Turai, amma yanzu ba zato ba tsammani ya zama dodon raga da har ake kwatanta shi da zaratan 'yan wasa irinsu Lionel Messi da Cristiano Ronaldo?

Wani lokaci, yana taimaka wa idan dan wasa ya samu kan shi a inda ya dace da kuma lokacin da ya dace, ko dai tun a makarantar kwallon kafa ta Masar ko kuma a wasu manyan 'yan wasa na gasar Firimiya.

Lokacin da Liverpool ta sanar da karbo Salah daga kulub din Roma na Italiya a bara, wasu da dama na ganin kudin da aka karbo dan wasan fam miliyan 55.7 sun yi yawa ga dan wasan da ya kasa nuna kansa a Ingila lokacin yana Chelsea a 2015.

Wani abu muhimmi da ya kamata a sani shi ne, duk da cewa Masar ba ta yi fice ba a duniya, amma uwa ce a Afirka domin ta lashe kofin nahiyar sau bakwai.

Sau biyu kawai Masar ta buga gasar cin kofin duniya a (1934 da 1990) da kuma yanzu zamanin Salah, inda ake ganin za su mamaye kanun labarai musamman mai tsaron raga Essam El-Hadary da zai kasance dan wasa mafi tsufa da ya buga a gasar da Masar za ta buga a Rasha.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sau biyu Masar ta je gasar cin kofin duniya kafin wannan da za a yi a Rasha

Shin tun a farko wacce matsala Salah ce ya fuskanta a Ingila? Salah ya taba taka-leda a Switzerland, inda ba za a iya hada lig din kasar ba da gasar Firimiya ta Ingila.

A lokacin da yana Chelsea, ya fuskanci kalubale na hammaya tsakanin shi da 'yan wasan Chelsea inda ya gaza samun wata babbar dama da zai iya burge Jose Mourinho.

Wasanni 19 kawai dan wasan na Masar ya buga wa Chelsea - An fara wasa da shi sau tara. Sau biyu kawai ya yi minti 90 a fili.

Sau biyu ana ba da aronsa a kungiyoyin biyu na Italiya kafin ya kulla yarjejeniya da Roma kakar 2015/16.

A Roma ne Salah ya nuna kansa inda ya ci kwallaye 34 a kaka biyu, matakin da ya sa ya samu damar zuwa Liverpool.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Abubuwa ba su tafi yadda ya kamata ba ga Salah a Chelsea

"Yana matashinsa ko da ya zo Chelsea. Kuma lokacin Chelsea tana da manyan 'yan wasa, don haka abu ne mai wahala," kamar yadda kocin Liverpool Jurgen Klopp ya shaida wa wata kafar talabijin ta Jamus.

"Ina ganin kowa zai yarda cewa Jose Mourinho babban koci ne, kuma wani lokaci abubuwa sukan kasance haka. Idan ta ki ka anan sai ka sake gwada wa a wani wurin - abin da ya faru ke nan da Mohamed."

A ziyarar da ya kai kwana nan a Anfield, Mourinho wanda yanzu shi ne kocin Manchester United, an nuna shi ya rungume Mohamed Salah.

Sannan a wata hira da kafar ESPC ta yi da shi, Mourinho a karon farko ya yi bayani game da alakarsa da dan wasan.

"Ni ne na karbo Salah kuma ba ni ba ne dalilin sayar da shi, illa Chelsea. Ina ma shi farin ciki, musamman saboda bai ci United ba a kakar bana, kamar yadda Mourinho ya fada a cikin raha.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Abubuwa sun sauya wa Salah a Liverpool

A wasa 50 da ya buga wa Liverpool, dan wasan na Masar ya zura kwallo 44 a raga tare da taimaka wa aka ci 15. Ya taka muhimmiyar rawa ga nasarar Liverpool a gasar zakarun Turai inda ya taimaka wa kungiyar ta kai wasan karshe a karon farko tun 2007.

Daya daga cikin tarihin da Salah zai kafa shi ne zai kasance dan wasan Afirka na farko da ya lashe kyautar wanda ya fi yawan cin kwallaye a Turai.

Rawar da zai taka a gasar cin kofin duniya za ta taimaka ma sa, baya ga wasan karshe na gasar zakarun Turai.

A wasannin samun gurbin zuwa gasar cin kofin duniya, Salah ya zura wa Masar kwallo biyar a raga, daya daga cikin bajintarsa sun hada da kwallon da ya ci a bugun fanariti a ragar Congo wanda ya taimakawa kasarsa zuwa gasar ta Rasha.

Ana minti 94 da wasa ne Salah ya ci Congo a wasan zangon karshe na neman zuwa Rasha.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Salah ya ci kwallo biyar a wasannin Masar na neman zuwa gasar cin kofin duniya

Samun dan wasa mai tawali'u kamar Salah zai yi wahala musamman a zamanin da cin kwallo a raga ne gaban 'yan wasan da suka mallaki miliyoyin kudi - Halayensa na Musulmi - sun kara ma sa farin ji ga magoya baya da kafofin yada labarai.

Dan wasa ne da Misrawa suke matukar girmamawa musamman a daidai lokacin da rikicin siyasa ya raba kasar.

Ya dauki nauyin gina makaranta da asibiti tare da bayar da tallafin kudi dala 280,000 ga shirin gwamnati na raya rayuwar talakawa a Masar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Salah ya taba taka leda a Basel a 2012

Wani abu daya na suka da ke tattare da Salah shi ne zargin cewa yadda ya kauracewa shan hannu da 'yan wasan kungiyar Macabbi Tel Aviv ta Isra'ila a lokacin wasansu da Basel a 2013 - Ya tafi ya sauya takalminsa a lokacin da ya kamata ya gaisa da 'yan wasan.

A lokacin, 'yan kasar Masar da dama sun soki dan wasan, inda har sun so kada dan wasan ya buga karawa ta biyu a Isra'ila.

Amma duk da haka dan wasan ya buga wasan tare da jefa kwallo a raga a gaban magoya bayan Maccabi.

Bayan da Salah ya taimakawa Liverpool lallasa Roma 5-2 a wasan dab da karshe a gasar zakarun Turai, ministan tsaron Isra'ila Avigdor Lieberman ya wallafa wani sako na raha cewa zai "kira babban hafsan soji domin ya shaida ma sa cewa ya ba Mohammed Salah aiki na dindin a rudunar sojin Isra'ila."

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Salah gwarzo ne a kasar Masar - kuma ya kama hanyar zama gwarzo a duniya