Man Utd na son Toby Alderweireld da Fred

Toby Alderweireld and Fred Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dan wasan tsakiyar Tottenham, Toby Alderweireld da kuma dan wasan tsakiyar Shakhtar Donetsk Fred suna cikin 'yan wasan Manchester United ke hako

Manchester United ta yi tambaya game da dan wasan Tottenham Toby Alderweireld da kuma dan wasan tsakiyar Shakhtar Donetsk, Fred.

United za ta kashe sama da fam miliyan 100 kan 'yan wasan biyu saboda Kocin United Jose Mourinho yana neman karfafa bayan klub din.

United na fatan kammala yarjejeniyar sayen dan Brazil mai sunna Fred kafin gasar cin kofin duniya.

Tottenham na karfin gwiwar sayar da Alderweireld saboda zai iya barin kulob din kan kudi fam miliyan 25 cikin watanni 12.

A halin yanzu, Juventus na son dan wasan bayan United Matteo Darmian.

Dan wasan na kasar Italiya, mai shekara 28, yana da sauran shekara daya a kafin kwantiraginsa ya kare, kuma wasanni biyar kawai aka fara da shi a kakar gasar Firimiyar da aka kammala.

Tare da Daley Blind da kuma Luka Shaw, Darmian yana da makoma 'yar kadan ne a kulob din yayin da Mourinho, wanda ya sabunta kwantiraginsa a watan Janairu domin cigaba da zama a Old Trafford har zuwa akalla shekarar 2020, yake neman karfafa kulob dinsa.

United ta karkare kakar a mataki na biyu a gasar Firimiyar Ingila - matsayinsu mafi girma tun lokacin da Sir Alex Ferguson ya yi ritaya a shekarar 2013 - amma da maki 19 ne Manchester City, wadanda suka lashe gasar, ta fi ta.

Belgium defender Alderweireld and Brazil midfielder Fred have both been selected for their World Cup squads.

An zabi dan wasan Belgium Alderweireld da kuma dan watsan tsakiyar Brazil Fred a gasar cin kofin duniya.